Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga sabon Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD MANDAWARI

Zuwa ga Abba Kabir Yusuf, Bayan haihuwa mai yawa, da farko a madadina da iyalina bakiɗaya muna taya ka murnar samun nasarar cin zaɓen Gwamnan jihar Kano na wannan shekara ta 2023. Muna yi maka addu’a, Allah ya sa jihar Kano ta sami ci gaban da ba ta tava samu ba a zamanin mulkinka, kai kuma Allah ya sa ka fara lafiya ka gama lafiya alfarmar Shugaba sallallahu alaihi wa sallam, amin.

Na zaɓi na aiko maka da buɗaɗɗiyar wasiƙa ne a wannan wata mai alfarma na Ramadan kuma domin ina da shawarwari da zan ba ka, sannan ina ganin idan sauran na hannun damanka suka karanta wasiƙar, to za su dinga tunasar da kai yayin da ka shiga cikin gidan Gwamnati. Don haka ga shawarwarin kamar haka:

(1) Yankunan karkara:

Ina fata za ka kalli yankunan karkara ta fuskar samar musu da ababen more rayuwa domin ɗauke wa babban birnin jiha cunkoso, na tabbata in ka zaɓi wasu kananan hukumomi da ke ƙauyuka ka samar musu da abubuwan ci gaba kamar Asibitoci ma su ɗauke da isassun magunguna da ƙwararrun likitoci, to ka ɗauke wa ‘yan’uwanmu na karkara wahalar zuwa Asibitin Murtala ko sir Sunusi ko Nasarawa da sauransu.


Kazalika ka samar wa yankunan karkara da manyan kasuwanni na zamani da hanyoyi da ruwan sha da hasken wutar lantarki da makamantansu, sannan ka yi ƙoƙarin sakarwa ƙananan hukumomi da kuɗaɗensu na ‘ grant’. Na tabbata in ka yi haka za ka rage wa babban birnin jiha cunkoso da nauye-nauye wanda a yanzu yana cikin matsalar jihar Kano.

(2) Rarraba ayyukan gwamnati

A kwai buƙatar ka fito da tsarin da a turance ake cewa ‘de-centralization of authority’ wato rarraba nauye-nauyen gudanar da Gwamnati daga sama zuwa ƙasa, misali a nan shi ne, idan ka tsara biya wa yara tallafin karatu ko kai su ƙasashen waje domin karatu, ko kuma idan ka yi shirin bayar da jari ga Mata ko masu ƙananan sana’u, to yana da kyau ka bayar da dama a zavo waɗanda suka cancanta tun daga matakin mazaɓu zuwa matakin ƙananan hukumomi zuwa jiha, ta haka ne za a taimaki jama’a tun daga tushe (grassroot) kuma shirin Gwamnati (policy) na zai dinga tava talakawa kai tsaye, amma idan aka ce wata hukuma ko wani kwamiti ne zai dinga gudanarwa da ire-iren waɗannan tsare-tsare shi kaɗai a matakin jiha, to ba za a cimma nasara yadda ya kamata ba.

(3)Madatsun ruwa:

Ya mai girma Gwamna, ina ganin zai yi kyau a kalli manyan Madatsun ruwan nan na Kano (Dams) wadanda aka samar da su tun zamanin Gwamnan jihar Kano na farko wato Alhaji Abdu Bako da nufin bunƙasa noman rani da na Damina, amma an yi shakulatin ɓangaro da su shekaru masu yawa, tattare da cewa in aka ba su muhimmanci to za su bunƙasa tattalin arzikin manoma da makiyaya da ma na jihar gabaɗaya.

(4) Ayyuka masu gajeren zango, da matsakaicin zango, da kuma gajeren zango:

Haka ma ina ba da shawara da cewa Gwamanati ta fito da manyan tsare-tsaren da za su taimaki jihar Kano, amma ta rarraba su zuwa kashi uku: wato masu gajeren zango (short term plan) da ma su matsakaicin zango (medium term plan) da kuma ma su dogon zango (long term plan).

Misalin irin wadannan su ne:

(i) Gajeren zango: Misalinsa shi ne kamar: kawar da shara, samar da magunguna, samar da abinci ga ɗalibai da ire-irensu, domin su waɗannan suna cikin shirye-shiryen da a kullum ake buƙatarsu.

(i) Masu matsakaicin zango:
Ire-iren waɗannan su ne kamar: samar da guraren kwashe shara ɗin na dindindin musamman a birane, da biyan kuɗaɗen WAEC da NECI ko kai ɗalibai ƙasashen waje da makamantansu, domin kuwa wannan ba kullum ake ba amma za a iya ganin alfanunsu ba da daɗewa ba.

(i) Mai dogon zango: Su ne kamar samar da kamfanonin da za su sarrafa shara domin su zama taki ko wani abin amfani kamar dai yadda ake yi a sauran ƙasashen Duniya, haka ma gina ƙananan asibitoci na daga cikin ayyuka masu dogon zango da dai makamantan waɗannan.

Ina ganin idan an bi ayyukan Gwamnati zango-zango to zai sa Gwamanati ta tafi a nutse ba tare da ta gigice har ta rasa me za ta yi ba.

(5) Masarauta:

Ina ganin Masarauta na da muhimmiyar gudanarwar da za ta bayar wajan samun nasarar shirye-shiryen Gwamnati. Wannan na nufin a dinga neman shawarar Masarauta musamman in za a zo da wani sabon tsari (new policy) da ya shafi al’umma kai tsaye; misalin irin waɗannan su ne kamar matsalolin da suka shafi aure ko tarbiyyar matasa ko yaƙi da shaye shaye ko dabanci da makamantansu. Na tabbata Masarauta na da kyawawan shawarwari ga duk wadannan matsaloli da dangoginsu kasancewar sarakunan gargajiya na kusa da Talakawa fiye da jami’an Gwamnati. Na faɗi hakan ne domin akwai shirye-shiryen Gwamnati da ba su samu nasara ba sai da aka haɗa da masarauta; misali shirin nan na ɗigon polio ba su sami karɓuwa sai da Sarki da Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni suka tallafa.

(6) Hanyoyin Sadarwa:

Hanyoyin sadarwa na zamani na buƙatar kulawa ta musamman domin ta zamar wa al’ummar wannan zamani alaƙaƙai, ma’ana dole rayuwa ba za ta yi wu ba sai an haɗa da hanyoyin sadarwa na zamani da na gargajiya, illa dai sai an fahimci alfanun da rashin alfanun da ke kunshe cikin hanyoyin sadarwar na zamani (social media) tukuna sannan za a ci gajiyarsu. Kowa ya san daya daga cikin hanyoyin da ake shigar da fajirce da rashin tarbiyya tsakanin matasa ita ce ‘Soshiyal midiya’.

Dan haka akwai buƙatar a samar da cibiyar horaswa a kan soshiyal midiya domin koyarwa da wayar da kan matasa domin su gane cewa ba wai sakarci ake yi a soshiyal midiya ba, a’a, ana iya gudanar da kasuwancin da za a iya samun miliyoyin kuɗi idan an koyi yadda ake yi.

A nan ina bai wa mai girma Gwamna shawara cewa a sauya fasalin Hukumar tace fina-finai domin yi mata sabbin dokokin da za su dace da wannan zamani na ‘soshiyal midiya’ alabashi a shigar da batun Soshiyal midiya ɗin nan cikin sabbin dokokin. Yin hakan ya zama dole domin a yanzu akasarin dokokin Hukumar ba su dace da wannan zamani ba tunda an yi su ne a lokacin da babu ƙalubalen soshiyal midiya.

(7) Sana’o’in hannu:

Akwai buƙatar a raya sana’o’in hannu musamman idan an zo ’empowerment’. Wannan yana da muhimmanci domin kuwa na lura a kan bar sana’o’in da suke da matuƙar muhimmanci wajen bunqasa tattalin arziki. A nan ina la’akari da sana’o’in teloli da masu aikin lantarki da masu aikin famfo da masu fanti da ‘yan walda da ire-irensu, kazalika akwai sana’o’in gargajiya irin su alkaki da nakiya da gireba da dubulan da makamantansu, har ila yau, akwai sana’o’i irin su gyaran waya da aski da makaneza da graphics da aikin komfuta da sauransu.

To amma a nan dole sai an sake tsari wajan zaɓar matasan da suka dace da kowace sana’a, ba lallai ‘yan jam’iyya ba, sannan a empowerment da su horo na gaskiya ba wanda za a nuna midiya a ce an yi ” ba.

Ƙarshe ina fata ba za ka bari mugayen fadawa su dinga ba ka muguwar shawara ba. Sannan ban da ramuwar gayya, domin yanzu kai uban kowa ne.

Muna ƙara yi maka addu’ar Allah ya yi riƙo da hannunka amin summa amin.

Ibrahim Muhammad Mandawari
(Maiunguwar Mandawari)
kuma mai kishin ci gaban wannan jiha ta Kano.
gsm: 234 8036191909
email: [email protected]

By Editor