An tsinci gawar mai ciki a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An tsinci gawar wata mai ciki mai shekara 20 a gefen titi a ƙauyen Anadariya da Ƙaramar Hukumar Bebeji ta jihar Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana haka a ranar Talata, inda ta ce an tsinci gawar ne a ranar 28 ga watan Maris.

A cikin wata sanarwa da Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce an cafke wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan matar.

Ya ce kamen na zuwa ne kwanaki kaɗan da kisan nata bayan da wasu mazauna yankin suka shigar da ƙara kan lamarin kuma Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mamman Dauda, ya tura jami’an ‘yan sanda wurin.

“Da samun rahoton faruwar lamarin Kwamishina Mamman Dauda ya aike da tawaga wajen ƙarƙashin jagorancin SP Tanimu Wada da ke ofishin ‘yan sandan na Bebeji.

“Bayan isa tawagar sun ɗauki gawar zuwa Babban Asibitin Tiga, wanda a nan aka tabbatar da rasuwarta.”

Kakakin ya ce an gano sunan matar a matsayin Theresa Yakubu, kuma an cafke saurayinta da abokinsa.

Saurayin nata ya amsa cewar sun kashe ta shi da abokinsa bayan ya yi mata ciki, kuma sun yi yunƙurin zubar da cikin amma abun ya ci tura.

A nasa ɓangaren Kwamishinan ‘yan sandan ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayiyar sannan ya tabbatar musu da yin adalci a kan lamarin.

Sannan ya yi kira ga al’umma da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanai don ganin an kamo waɗanda ake zargi.

Daga nan Kwamishinan ya bada umurnin maida binciken zuwa Sashin Bincike na Manyan Laifuka da ke Bomfai domin zurfafa bincike.