APC a Delta ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga jam’iyyar

Daga WAKILINMU

Jam’iyyar APC ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege daga jam’iyyar kamar yadda rahotanni suka nuna.

Da fari rahotanni sun nuna yadda APC a Jihar Delta ta kori Omo-Agege daga jam’iyyar cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Maris da kuma sa hannun Shugaban jam’iyyar na jihar, Ulebor Isaac a madadin shugabancin jam’iyyar a jihar.

An ce sun ɗauki matakin korar ne bayan da suka zarge shi da yi wa jam’iyyar zagon ƙasa da sauran laifuka waɗanda ba a bayyana ba.

Sai dai kuma, tsagin APC a jihar da ke yin Mataimakin Shugaban Majalisar ya yi fatali da korar da aka ce an yi masa.

Cikin sanarwar da shugabancin tsagin APC mai mara wa Omo-Agege baya ya fitar a ranar Litinin, sun ce su ne doka ta sani a matsayin shugabannin APC a jihar amma ba wancan ɓangaren ba.