Rikicin Sudan: Saudiyya ta zama ƙasa ta farko wajen kwashe ‘ya’yanta

Daga BASHIR ISAH

Wani jirgin ruwan Ƙasar Saudiyya ya isa Jidda bayan da ya yi jigilar ‘yan ƙasar da suka maƙale a Ƙasar Sudan sakamakon rikicin da ƙasar ke fama da shi.

A cewar tashar talabijin ta Jidda, “Jirgin ruwan farko da ya kwaso ‘yan ƙasar daga Sudan ya isa gida ɗauke da mutum 50 tare da wasu daga maƙwabtan ƙasar.”

Bayanai sun ce an hangi wasu jiragen ruwa na ƙasashe daban-daban a Kogin Maliya ɗauke da mutum 108 daga Sudan wanda ake sa ran su isa ƙasashensu ba da jimawa ba.

Wannan nasarar da Saudiyya ta samu ya sa ta zama ƙasa ta farkon da ta yi nasarar kwashe ‘ya’yanta daga Sudan zuwa gida tun bayan da rikici ya ɓalle a ƙasar a ranar 15 ga Afrilu.