Ingila ta yi sabon Sarki bayan shekaru 70

*Sarki Charles na III ya gaji mahaifiyarsa

Rahotanni daga ƙasar Ingila sun ce, an gudanar da gagarumin bikin naɗin Sarki Charles na III a wannan Asabar, inda Arcbishop na Canterbury ya sanya masa kambin sarautar Ingila domin maye gadon mulki na marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Bikin, shi ne irinsa na farko cikin shekaru 70 da suka gabata.

An gani tare da jin yadda mahalartar bikin suka ɓige da sowa a yayin sanya wa Sarkin kambin sarauta na zinari wanda aka samar da shi tun a ƙarni na 17.

Tun bayan da aka gudanar da makamancin wannan biki a shekarar 1937 sa’ilin da aka naɗa mahaifiyar Sarki mai ci, Sarauniya Elizabeth, sarauniyar Ingila, hakan bai sake aukuwa ba sai a wannan karon.

Dubban mutane ne suka yi dandazo a tsakiyar birnin London domin shaida naɗin sarautar Sarki Charles III.