Daga AMINA YUSUF ALI
Fitaccen jarumin nan na Kannywood da Nollywood, Usman Uzee, ya zama jakadan bankin nan na Musulunci, wato TajBank.
A ranar Alhamis, 4 ga Mayu, 2023, jarumin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da bankin tare da manyan jami’an bankin.
Idan dai za a iya tunawa, bankin na TajBank yana daga cikin kalilan din bankuna a Nijeriya da ba su mu’amula da kudin ruwa.
Shi kuwa Jarumi Uzee yana daga kalilan din jarumin Nijeriya da suke fitowa a finafinan Arewa da na Kudu. Daya daga cikin fitattun finafinan da ya fito shine, Voiceless, wanda ya samu hawa manhajar NetFlix.
Ga ƙarin hotuna:

