Za mu ci gaba da tuna ‘Yar’adua saboda cigaban da ya kawo wa Nijeriya – Jonathan

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidansa, Umaru ‘Yar’adua, a matsayin shugaba maras son zuciya.

Ya bayyana haka ne a wani ɓangare na ranar cika shekara 13 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar na Nijeriya.

Jonathan ya kasance mataimakin Umaru Musa ‘Yar’Adua daga 2007 zuwa 2010

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita ranar Juma’a, inda ya ce, “A wannan rana shekara 13 da ta wuce, ƙasarmu ta yi rashin gawurtaccen shugaba maras son zuciya, Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.”

Mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta gaskiya kamar yadda BBC ta rawaito.

“Muna waiwaye don nuna godiya ga Allah saboda rayuwarsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga ƙasarmu.

“Shugaba Yar’Adua, jagora ne abin misali, wanda ya rayu ba tare da nuna bambancin ƙabilanci ko na addini ba. Kuma gudunmawarsa a fagen aikin gwamnati ta zaburar da mutane da yawa kan hanyar alheri.

“A yau, muna tuna shi da kuma hidimar da ya yi a rayuwarsa da jajircewa da duƙufa wajen tabbatar da dunƙulalliyar ƙasa ɗaya mai bunƙasar arziƙi.”

Goodluck Jonathan ya ce: “Za mu ci gaba da tunawa da shi saboda gagarumin cigaban da ya kawo da kuma himmarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban Nijeriya”.