Yadda aka gudanar da addu’o’in tunawa da ‘Yar’adua bayan cika shekara 13 da rasuwa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gamayyar ƙungiyoyi masu goyon bayan jam’iyyar PDP, sun shirya taron addu’a gami da karatun Al’ƙur’ani mai girma don tunawa da tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua a masallacin hedikwatar jam’iyyar PDP dake Katsina.

Taron addu’o’in na zuwa ne bayan da marigayi ‘Yar’adua ya cika shekaru 13 da rasuwa a ranar Juma’a, 5 ga watan Mayu, 2023.

Da yake jawabi a wajen taron addu’ar, Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar wanda ya samu wakilcin Lawal Rufa’i Safana, ya bayyana cewar, shirya taron addu’o’in ya zama wajibi duba da gagarumin cigaba da marigayin ya kawo wa ƙasar nan lokacin da yake mulki, inda ya haɓaka tattalin arziƙin ƙasa, haɗin kai gami da ɗorewar cigaba da kasancewar Nijeriya a matsayin ƙasa.

Saboda haka ne, ya bayyana cewar ‘yan Nijeriya ba za su taɓa mantawa da shi ba saboda gudummawar da ya bai wa ƙasa a halin rayuwarsa.

Shi ma a na shi jawabin, mai riƙon muƙamin Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Hon. Hamza Yunusa Jibiya, ya bayyana marigayi ‘Yar’adua a matsayin uba, wanda ya kamata a yi koyi da shi, kuma shugaba mai gaskiya gami da hangen nesa.

Hon. Yunusa ya ƙara da cewa, akwai buƙatar shugabannin Nijeriya na yanzu da kuma masu zuwa nan gaba da su yi koyi da shi wajen shugabanci nagari.

Sheik Malam Mani Gambarawa ne ya jagoranci taron addu’ar, inda ya yi addu’ar Allah Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomar marigayin.