WAEC ta bayyana ranar da za a yi jarrabawar 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta sanar da cewa za a gudanar da jarrabawar kammala Sakandare ta Yammacin Afirka ta 2023 (WASSCE) na tsawon makonni bakwai, tsakanin 8 ga Mayu zuwa 23 ga Yuni, 2023.

Shugaban hukumar na ƙasa, Patrick Areghan ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai gabanin jarrabawar a Legas a ranar Alhamis, 4 ga Mayu, 2023.

Areghan ya ce, jarabawar za ta ƙunshi mutane 1,621,853 daga makarantun gwamnati da masu zaman kansu 20,851.