An kashe Gwamnan Afghanistan a harin bom

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga yankin Arewacin Afghanistan sun ce, an kashe gwamnan riƙo na yankin a wani harin bom da aka kai ta hanyar amfani da mota.

Wannan shi ne makamancin harin da aka yi amfani da shi wajen kashe wani babban jami’in ɗan sanda a yankin, harin da mayaƙan ISIL (ISIS) suka ɗauki alhakin kaiwa.

An ce maharin ya shigi motar Nisar Ahmad Ahmadi da motarsa mai ɗauke da bom wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar muƙaddashin gwamnan Arewacin Badakhshan a ƙasar.

Bayanai sun ce direban motar ya mutu yayin da wasu mutum shida sun jikkata.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu cikakken bayani a kan ko su wane ne suka kai harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *