Gwamnan Lawal ya bai wa hukuma umarnin gaggauta magance matsalar ƙarancin ruwa a Gusau

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bai wa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar umarni a kan ta gaggauta samar da ruwa a Gusau, babban birnin jihar domin ceto al’ummar yankin daga matsalar ƙarancin ruwan da suke fuskanta.

Dauda ya ba da umarnin haka ne ta bakin wakilinsa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Hon. Mukhtar Lugga, yayin da ya kai ziyarar ba-zata a ma’aikatar a ranar Talata.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Sadarwa, Nuhu Salihu Anka ya raba wa manema labarai a birnin.

A cewar sanarwar, “Ana sanar da al’ummar jihar cewar Mai Girma Gwamna Dauda Lawal ya damu matuƙa game da matsalar ƙarancin ruwan da al’ummar Gusau da kewaye ke fuskanta.

“Wannan ya sa Gwamnan ya kai ziyarar ba-zata Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar wadda ta yi ƙarin haske kan matsalar rashin ruwan da ake gama da ita a yankin.

“Kuma nan take Gwamnan ya bai wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Hon. mukhtar Lugga umarnin ya haɗa kai da hukumar ma’aikatar domin gaggauta samar da ruwa ga al’ummar Gusau da kewaye.”

Gwamnatin Zamfara ta ce za ta bai wa ma’aikatar gudunmawar da ta dace domin shawo kan matsalar.