Mu shiryawa ganin canje-canje a sabuwar gwamnati

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Babu shakka dimukraɗiyyar Nijeriya tana ƙara samun gindin zama da bunƙasa sosai. A tsawon shekaru 23 da komawa kan turbar dimukraɗiyya daga shekarar 1999, Nijeriya ta samu sauye-sauye da dama a ɓangarorin tafiyar da sha’anin mulki, harkar tsaro, manyan ayyukan raya ƙasa, da bunqasa harkokin lafiya da ilimi, da kuma uwa-uba cigaban walwalar jama’a. Ba za a ce komai ya tafi daidai ba, an fuskanci ƙalubale iri-iri da suka haɗa koma bayan tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa, rikice-rikicen ƙabilanci da ta’addanci, da cin hanci da rashawa, amma duk da haka za a ce kwalliya tana biyan kuɗin sabulu.

Lallai babu shakka, idan muka waiwaya baya muka dubi shekarun da suka gabata kafin 1999, za mu ce lallai an samu cigaba. Ko babu komai yadda ake samun damar yin zaɓe bayan kowanne shekaru 4, da kuma miƙa mulki ga sabbin shugabannin da aka zaɓa, cikin nasara da kwanciyar hankali ba tare da yaƙi ko jayayya mai zafi ba, wannan ma babbar nasarar dimukraɗiyya ce. Don kuwa idan muka dubi wasu ƙasashen Afirka ko ƙasashe masu tasowa da za a iya haxa tafiyar su da Nijeriya, lallai za a ce sambarka, Nijeriya ta cimma nasarori.

An shiga zango na biyar kenan na shugabannin ƙasa da aka zaɓe su a ƙarƙashin mulkin dimukraɗiyya, da suka haɗa da Cif Olusegun Obasanjo, Umaru Musa ’yar’adua, Goodluck Jonathan, Muhammadu Buhari, da kuma sabon shugaban ƙasa na yanzu Bola Ahmed Tinubu. Biyu daga cikinsu sun taɓa riƙe ƙasar a ƙarƙashin tsarin mulkin soja, wato Obasanjo da Buhari.

Ɗaya bayan ɗaya za mu iya cewa, kowannensu ya taka rawar gani wajen kafa wani tsari da za a tuna da shi, kuma zai kawo sauyi a ƙasa. Wasu tsare-tsaren nasu sun zo da sauƙi wasu kuma an sha wuya. Sai dai ta kowacce fuska idan ka kalli abin za ka fahimci lallai, an kawo tsarin ne da kyakkyawar manufa, kuma don cigaban ƙasa ne da rayuwar ’yan Nijeriya. Wasu tsare-tsaren an samu nasara wajen gudanar da su, wasu kuma wajen aiwatarwa akan yi ta samun tuntuve.

Yanzu dai tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma jagoran Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya zama shugaban ƙasa mai cikakken iko, bayan ya yi rantsuwar kama aiki. Sai dai wata tataɓurza ta biyo bayan jawabinsa na ranar rantsarwa sakamakon sanarwar da aka ji daga bakin sa, cewa gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur. Batun da ya kaɗa hantar ‘yan ƙasa, kuma ya jefa ƙasa cikin ruɗani.

Ƙasa da awoyi 48 da karɓar mulki, har an fara shiga doguwar tattaunawa da ƙungiyar ’yan ƙwadago ta NLC ƙarƙashin jagorancin Joe Ajaero da kuma shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ’yan kasuwa masu zaman kansu ta ƙasa TUC, Festus Osifo, da kuma kakakin fadar shugaban ƙasa, Dele Alake. Sai dai bayan shafe tsawon awoyi ana musanyen yawu, an tashi baram baram, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago ke buƙatar gwamnati ta janye batun ƙudirinta na cire tallafin man fetur, a dawo inda ake, don tattaunawa kan hanyoyin samun mafita. Ita kuma gwamnati na nuna cewa, babu komawa baya.

Kodayake tun kafin Tinubu ya karɓi ragamar tafiyar da ƙasar gwamnatin da ta gabata ta yanke shawarar janye ba da tallafin man fetur, don haka ma aka ce ba a shigar da batunsa cikin kasafin kuɗin bana ba. Amma kasancewar shi ne aka fara jin zancen daga bakinsa, ya sa wani ɓangare na ’yan qasa kokawa da sabuwar gwamnatin Tinubu, da tunanin shi ne ya shigo da salon muzgunawa ’yan Nijeriya. Har wasu na cewa, kada fa a fara cewa gwanda jiya da yau!

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rubutun, farashin man fetur ya tashi daga lita ɗaya a Naira 185 zuwa lita ɗaya ta man fetur Naira 400 har 600 a wasu wuraren. Wannan ya jawo ƙaruwar dogayen layukan ababen hawa a gidajen man da suka yarda za su sayar, yayin da wasu gidajen man ma rufewa kawai suka yi. Saboda kaucewa hayaniyar da ta taso, da kuma tursasawa gwamnati ta hanyar haifar da ƙarancin man fetur. Tuni farashin wasu kayan masarufi ya yi tashin gwauron zavi, kuɗin abin hawa na zirga-zirgar cikin gari, da na motocin babbar hanya, shi ma yana neman ninka farashin baya, kafin hawan Tinubu.

Babu shakka bakin ’yan Nijeriya ya rabu biyu, game da wannan batu mai sarƙaƙiya. Yayin da wasu ke kiran a yi wa gwamnati uzuri, saboda da ƙalubalen da ke jiranta, da masu ganin, idan aka yi shiru a haka za a faɗa cikin baƙar wuya, rayuwa za ta ƙara tsada, talaka zai sake ɗanɗana kuɗarsa. Daga cikin masu goyon bayan gwamnati, akwai masanin harkokin siyasa, Reno Omokri da ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa, masu sukar tsohon shugaba ƙasa Buhari, kan bashin da yake ta karɓa da sunan Nijeriya har zuwa dab da saukar sa a mulki, ba su san sirrin halin da ƙasar nan ke ciki ba ne. Ya ƙara da cewa, kuɗaɗen da ake karɓowa bashi, da su ne ake biyan kuɗaɗen tallafin man fetur, abin da ya kamata a ce an yi amfani da su ne a ayyukan raya qasa da su.

Wannan na daga cikin irin tuntuɓen da na yi magana a baya, wajen tafiyar da wasu tsare tsaren da gwamnati ke ɓullo da su. Dubi dai yadda sabuwar gwamnati ta fara karyawa da tofin Allah-tsine daga bakin talakawan da suka zaɓe ta kuma suka riƙa yi mata addu’ar Allah ya sa da alheri ta zo.

Abin takaici ne duk lokacin da Gwamnatin Tarayya ta yunƙuro don daidaita al’amura da ƙoƙarin ganar da ’yan Nijeriya game da muhimmancin cire tallafin man fetur ɗin nan, sai ƙungiyoyin dillalan man fetur ɗin nan su yi ta amfani da damar da suke da ita na dakatar da sayar da man fetur da tsawwala farashin sa a kasuwannin bayan fage, wanda hakan zai sa farashin abin hawa da na kayan masarufi ya tashi, jama’a kuma su shiga wahala. Daga nan sai ƙungiyar ma’aikata ta NLC ta fito su tana ƙalubalantar gwamnati, don ta janye matakin da ta ɗauka.

A nan ba ina goyon bayan janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi ba ne, amma ina bayyana cewa ba kowanne lokaci ne wasu tsare-tsaren gwamnati suke zuwa wa talakan Nijeriya da sauƙi ba, amma idan aka yi haƙuri sai ka ga sun zo da wani alheri da za a amfana. Masana dai na ganin matuƙar gwamnati za ta cika alƙawarin da ta yi wa ‘yan Nijeriya na amfani da biliyoyin kuɗaɗen da za ta karkatar da su daga biyan tallafi zuwa ga ayyukan raya ƙasa to, babu shakka za a ji daɗi sosai. Kuma alƙawarin da Shugaba Tinubu ya yi wa ’yan Nijeriya kafin hawansa mulki, cewa za su sha jar miya, kuma za a sarara daga ƙuncin da ‘yan Nijeriya suka shiga a baya, sakamakon wasu tsauraran matakan da gwamnatin da ta gabata ta ɗauka, don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.

Lallai ‘yan Nijeriya su ƙara jan ɗamara sosai, kuma su shiryawa ganin wasu ƙarin canje-canjen da za su vullo daga wannan gwamnati, bisa irin nata salon jagorancin, da kuma aiki da shawarwarin ƙwararru kan tattalin arziki da sauran vangarorin rayuwa. Sannan mu yi addu’a, mu roƙi Allah ya kawo mana sassauci, kuma ya ba mu zuciyar haƙurin duk wata jarabawa za ta tunkaro mu, da duk wani sauyi da za mu gani. Fatan mu gwamnati ta zo da sabbin dabaru na zamani don bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da al’umma baki ɗaya.