Gwamna Lawal ya nemi haɗin kan NADDC don horar da matasan Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya nemi haɗin kan cibiya ƙirƙire-ƙirƙire tsarin motoci ta ƙasa, wato NADDC da ke Abuja, domin horar matasan Jihar Zamfara da zimmar kyautata rayuwarsu.

Lawal ya buƙaci hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar cibiyar a ranar Talata, inda ya samu tarba daga Shugaban cibiyar, Jelani Aliyu tare da wasu manyan jami’ansa.

Gwamnan ya ce a shirye Jihar Zamfara take don haɗa kai da cibiyar NADDC wajen bai wa matasan jihar ilimin da za su iya dogaro da kansu a rayuwa.

Wannan bayani na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labaran da Babban Hadimin Gwamnan kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Laraba.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Lawal ya ce, “A yau, mun zo ne domin neman damammakin da za su ƙara wa jiharmu ta Zamfara ƙaimi.

“Gwamnati ta gano fannoni masu muhimmanci da suka haɗa da tsaro da harkar ilimi da harkar noma da koyar da sana’o’i da kuma bunƙasa matasa.

“Na fahimci cewar NADDC ta buɗe cibiyar ba da horo a Gusau wadda ba rigada an ƙaddamar da ita ba. Gwamnatina za ta ba da dukkanin gudunmawar da ake buƙata domin tabbatar da an ƙaddamar da cibiyar da kuma fara aiki cikin nasara.”

A nasa ɓangaren, Shugaban NADDC, Jelani Aliyu, ya bayyana ziyarar Gwamnan Lawal a matsayin wata babbar alama da ke nuni da kyakkyawan shirin da sabuwar gwamnatin Zamfara ta yi.

Ya nuna farin cikinsa da godiya dangane da tabbacin da ya bai wa cibiyar na samun cikakken goyon bayan gwamnatin jihar.

Ya ƙara da cewa, cibiyar ba da horon wuri ne na ba da horo a ɓangarorin da suka shafi bincike da duba lafiyar motoci da sauransu.