Sana’a ga mace na wanzar da zaman lafiya a aurenta – Farida Musa Kalla

“Rashin sana’a ga matasa babbar illa ce ga al’umma”

Daga AISHA ASAS

Har zuwa yanzu ba a daina samun al’ummar da ke nuna ƙyara da tsangwama ga matan da suka yunƙura don neman na kansu a Ƙasar Hausa ba. Wasu kan la’ance su don irin sana’ar da suka zaɓa, wadda suke ganin bata dace da su ba a matsayin ‘ya’ya mata ba, yayin da wasu ke yin kuɗin goro kan mata masu neman na rufa wa kai asiri, wato matan da ba su da kamun kai ne kawai ke fita nema. Duk da wannan matan da suka san ciwon kansu ba su bari wannan ƙalubalen ya zama hujjar zaunewa a gida suna zaman kashe wando ba, sai dai sun yi dogon tunani don samar wa kansu maslaha, ta hanyar zaɓo sana’ar da ta yi daidai da su, wadda zata kare mutuncin su na mata. A wannan mako kamar kowanne lokaci, shafin Gimbiya ya yi wa masu karatu babban kamu, wadda muke da tabbacin mata da yawa za su ƙaru da irin rayuwa da matakan da ta taka da suka isar da ita ga nasara. Hajiya Farida Musa Kalla, jajirtacciyar mace ce, da ta iya haɗa taura biyu a lokaci guda ta taune. Mai ilimi ce da ta ba wa boko dama sosai a ƙwaƙwalwarta, domin ta mallaki digiri a ɓangaren Tattalin Arziki, duk da haka, bata tsaya jiran kammala karatu don cin moriyarsa ba, Hajiya Farida ta duƙufa neman na kanta ta hanyar kasuwanci, wanda a halin yanzu ta ke cin moriya. A tattaunawarta da Manhaja, mai karatu zai ilimintu da ababe da dama musamman ta ɓangaren kasuwanci da sauran batutuwan da muka tattauna da ita.
Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Hajiya Farida Musa Kallah:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki.

HAJIYA FARIDA : Assalamu alaikum. Sunana Farida Musa Kallah. An haife ni a unguwar Gwammaja da ke Jihar Kano. Na yi karatuna na firamare a Model Nursery and Primary da ke Sharaɗa, sannan na yi sakandare a Saint Louis secondary school. daga nan kuma na wuce Jami’ar Kano, inda na soma da difiloma a ‘Banking and Finance’, daga nan na ɗora da BSc a vangaren Tattalin Arziki, wato Economics. Na yi bautar ƙasa a asibitin ƙashi ita ma dai a cikin Jihar Kano, wato asibitin ƙashi da ke Dala.

Ina da aure kuma Allah Ya azurta ni da ‘ya’ya guda huɗu, mata biyu, maza biyu. Alhamdu lillah. Wannan shi ne tarihina a taƙaice.

A matsayinki ta mace ‘yar kasuwa da Allah Ya tarfa wa garinki nono ta fuskar kasuwanci, masu karatunmu za su so jin ta yadda ki ka fara wannan kasuwancin.

Alhamdu lillahi, zan iya cewa, na fara kasuwanci da ɗan kuɗi ƙalilan, domin na fara ne tun a lokacin da nake zuwa makaranta, ‘yan kaya kaɗan, waɗanda za ka iya riƙewa a hannu, ka siyar wa da ƙawaye da sauran abokanen karatu da suke zagayen ka.

Da irin haka na fara, har zuwa lokacin da na fara BSc, a lokacin Ina da aure, ba zan manta ba a shekarar 2010, mahaifiyata ta ba ni wasu kuɗaɗe da niyyar in siye mota, saboda samun sauƙin zuwa makaranta, saboda ga aure ga kuma haihuwa da na yi, to shi ne fa ta ba ni kuɗi dubu ɗari shida in samu motar zuwa makaranta.

To waɗannan kuɗin ne sai maigidana ya ga bai kamata a ce a take na siye mota da su ba, ya ce, na yi haƙuri da abinda muke da shi, idan lokaci ya yi da kansa zai siya min motar. Da wannan muka ajiye kuɗin har zuwa lokacin da nake bautar ƙasa. To a lokacin ne ya kawo shawarar me zai hana kuɗin na yi amfani da su na ƙara jari, na juya su , na dinga siyen ire-iren su atamfa, tunda ya ga sana’ar atamfar ya fi karɓa ta. Saboda kamar lokacin salla haka, zan iya siyar da atamfofi kamar ɗari haka, kuma akafar sada zumunta ta Fesbuk (Facebook) kawai, domin a lokacin ma babu irin su Instagram da sauransu.

Da wannan ne ya ga zan iya bunƙasa sana’ar da waɗannan kuɗin, domin idan har zan iya siyar da atamfa kusan ɗari a shafin sada zumunta, kuma ba bashi ba, to ina ga na haɗa da fita da su, tunda a lokacin Ina zuma asibitin ƙashi.

To a lokacin gaskiya ban so hakan ba, domin Ina ganin yin amfani da wannan kuɗin da nake ajiyewa kamar ba zai haifa min ɗa mai ido ba, kuma ma a lokacin jin kuɗin nake tamkar kuɗin cizo, saboda tsoron kar kuɗin su zo su lalace, kin san yadda farkon kowanne kasuwanci yake, akwai tsoron faɗuwa.

To fa sai da ya kwantar min da hankali kan cewa, idan kuɗin sun lalace shi zai biya ni, kuma a matsayin sa na ɗan kasuwa sai abin ya zo min cikin sauƙi, domin ya ɗora ni kan layi, don haka ban samu matsaloli masu yawa ba.

Kowacce sana’a tana tattare da qalubale. Ko akwai waɗanda ki ka samu a farkon fara kasuwanci?

Zancen ƙalubale kam sai dai mu yi hamdala, saboda a matsayina ta ‘ya mace kuma ‘yar Arewa, kuma yanayin sana’ar da nake yi sai ya kasance ba mata ne aka fi sani da ita ba. Babban ƙalubalen da na fuskata shi ne, kutsawa cikinsu don yin irin abinda aka fi sanin su da shi, sai na kasa ‘coping’, sannan su suka dinga yi min kallon baƙuwa, saboda ba abu ne da suka saba gani ba, to amma alhamdu lillahi, tafiya da ta yi tafiya ne sai suka haqura, suka amshe ni a matsayin ɗaya daga cikinsu.

Suka karɓe shi a matsayin canji ne ya zo, saboda idan kin yi duba da sana’ar a wasu jihohi kamar Iko, za ki ga sana’a ce ta mata, amma mu anan mazan ne aka fi sani da ita. kinga kuwa su baqo a can su ga namiji a kasuwa, mu kuma anan aga mace a kasuwa tana sana’a.

Idan na fahimce ki sosai, kuɗin da aka ba ki don siyan mota ne ya ƙarfafa kasuwancin da ki ke yi. Shin hakan ya zama alkhairi a gaba, ko kuɗin sun samu matsala?

Ƙwarai kuwa da gaske, hakan ya zama alkhairi, alhamdu lillahi, domin a cikin shekara ɗaya da fara juya kuɗin, zan iya cewa, na mayar da kuɗin, zan iya ma siyan mota a lokacin duk da cewa, farashin mota a lokacin ba ɗaya ba ne da lokacin da na yi niyyar siya. Don haka ya zama alkhairi gare ni sosai.

Kuma kinga ban samu matsala sosai a kasuwa ta ba, tunda kinsan dai babbar matsalar kasuwanci shi ne, bada bashi, yana matuƙar karyar d asana’a, to kinga ni ban fara da bashi ba, kuɗi-hannu nake nawa kasuwancin. Don haka ko da shekara ta zagayo, na samu alkhairi mai yawa da wannan kuɗin, kuma ga ƙarin cewa ba na buƙatar siyan mota a lokacin, saboda na san daɗin juya kuɗin, don haka na fi buƙatar su a kasuwancina.

Me za ki ce ga mata masu tasowa a yanzu da suka fi karkatar da hankalinsu kan saka kaya masu tsada ko riƙe manyan wayoyi alhali ba su da wata sana’a ko aiki da suke yi?

Gaskiya kam wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a tsakanin mata, ban sani ba ko don zamanin soshiyal midiya ne, don su saka, su nuna wa duniya suna sa manyan kaya ko suna riƙe babbar waya, wai duk dan a kalle su a matsayin wani abu. Wannan ɗabi’a ba qaramin illa ta ke yi wa al’umma ma gabakiɗaya ba, saboda sau da yawa za ki tarar masu wannnan ra’ayin sai sun yi da ƙyar suke yin wannan ƙarya.

Kiga matashi da babbar waya, amma yana neman na kuɗin abin hawa, ko na cin abinci. Yarinya bata sana’ar komai ta ƙuduri aniyyar mallakar waya ta maƙudan kuɗi, ina za ta same su, bata da shi, amma tana da niyyar aikata komai ma don cikar burinta, to daga wannan ne fa rayuwa ke fara hawa matakin lalacewa.

Ba wai na ce matasa kada su sa kayan ƙwarai ba, ko kada su riƙe manyan wayoyi ba, su yi haƙuri har matsayi ya kai su ga yin haka ba ƙarya ba. Kuɗaɗen da za ka siye wata waya, sun ishe ka jan jari, ka fara sana’a, ka sa haquri, har Allah Ya kai ka ga iya mallakar kowacce irin waya ko kaya. A lokiacin idan ka yi ba mai ganin laifin abin, don guminka ne ka ke ci. Abu mai muhimmanci a rayuwa shi ne, mutum ya koyi sana’a, ya dogara da kanshi, domin a cikin sana’a akwai albarka, don haka mai yin ta ba a taɓa kiran sa wanda bai san ciwon kansa ba.

Ko sana’a ga ‘ya mace na taka rawa a zaman aurenta?

Gaskiya sana’a a wurin ‘ya mace na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aurenta, sabina idan kina da sana’a Ina mai tabbatar miki auren ma sai ya fi ƙarko fiye da na wadda ke zaman kashe wando. Ga uwa uba kwanciyar hankali, ba ki da tashin hankalin matsala ta taso miki kina fargaban ko miji ya yi ma ki ko akasin hakan. Sanin kin fi ƙarfin buƙatunki kawai wani kwanciyar hankali ne da ba wadda ta sani sai wadda ta ɗanɗana.

Idan kuwa ki ka zama a jerin matan da suke kallon miji ga duk wata lalurar da zata taso masu, zan iya cewa, ko ba ni ba ni kawai ya isa ya hana aurenku walwala, kusan zan iya cewa, zaman lafiyarku ba zai wuce kaso talatin bisa ɗari ba.

Zan iya cewa sana’a tana taka rawa wurin haifar da zaman lafiya, shi kuwa zaman lafiya shi ne ginshiqin kowanne aure, domin da zaman lafiya ne kawai soyayya ke wanzuwa.

Ba mu labarin irin nasarorin da ki ka samu a ɓangaren kasuwanci kawo wa yanzu.

Da wannan tambaya za mu dasa aya, wadda baƙuwar tamu zata fara amsa mana ita a sati mai zuwa kafin sauran tambayoyin su biyo ba. Ku tsumaye mu zuwa sati mai zuwa, da yardar mai dukka za mu kai ƙarshen tattaunawarmu da Hajiya Farida Musa Kallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *