APC na zargin Kwankwaso da sayar da kadarorin Jihar Kano

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana cewa, tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya sayar da wasu filayen gwamnati da sauran kadarori sa’ilin da yake riƙe da jihar tsakanin shekarar 1999 da 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.

Kazalika, APC ta ce baya ga filayen gwamnati da aka sayar a sassan Kano, gwamnatin Kwankwaso ta sayar da wasu kadarorin gwamnatin jihar da ke Abuja da Legas.

Jam’iyyar ta yi zargin haka ne a wani taron manema labarai da ta shirya ranar Talata a sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya reshen Jihar Kano.

Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Shehu Maigari, ya ce babu mutuntawa game da rushe gine-ginen da gwamnatin Kano ke ci gaba da yi a jihar. Yana mai cewa, matakin ya tava harkokin miliyoyin ‘yan jihar.

A cewarsa, “Kasancewar Kano babbar cibiyar kasuwanci a Arewa da sauran ƙassashen Afirka, yanzu jihar na fuskantar masifa a ƙarƙashin gwamnatin NNPP.

“Matakin rushe wuraren neman abinci jama’a da gwamnatin ta ɗauka abu ne mai buƙatar addu’a daga jama’a, saboda waɗanda lamarin ya shafa na ƙirga miliyoyin Nairar da suka yi asara.

“Don haka muna kira ga waɗanda lamarin ya shafa da su yi haƙuri su kwantar da hankulansu sannan sun ɗauki matakin shari’a domin kare dukiyoyinsu da bin haƙƙin ɓarnar da aka yi musu.”