Akume ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Ƙwarya-ƙwaryar bikin rantsawar ya gudana ne ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, inda taron ya shaida yadda Akume ya sha rantsuwar kama aiki.

Mahalarta taron sun haɗa da: Mataimaki Shugaban Ƙasa Kashim Shettima; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan; Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, Shugaban Ma’aikatan Tarayya, Dr FolasadeYemi-Esan da sauransu.

Rantsarwa na zuwa ne kwana biyar bayan da Shugaban Ƙasa ya naɗa Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da kuma Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakinsa.

Tinubu ya bayyana naɗin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne yayin ganawar da ya yi da Ƙungiyar Gwamnoni ta Progressives Governors Forum (PGF) kwanan baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *