Tarihin rayuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An haife shi a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952 cikin birnin Legas.

Bola Tinubu Musulmi ne kuma ya halarci makarantar firamare mai suna St. John’s Primary School, da ke Aroloya da ke birnin Legas, sai sakandiren Children’s Home School da ke Ibadan.

Tinubu ya samu tafiya ƙasar Amurka domin ƙaro karatu a shekarar 1975, inda ya fara karatu a Kwalejin Richard J. Daley College da ke Chicago, Illinois kafin daga bisani ya koma jami’ar jihar Chicago mai suna Chicago State University.

Ya samu kammala digirinsa a shekarar 1979 daga wannan jami’ar inda ya karanci Ilimin Gudanarwar Kuɗi wato “Accounting”.

Tinubu ya yi aiki da kamfanin Amurka mai suna Arthur Andersen, da kuma wasu kamfanonin irinsu Deloitte, Haskins, & Sells, da GTE Services Corporation duk a can Amurka.

Bayan komowarsa gida Nijeriya a cikin shekarar 1983, Bola Tinubu ya soma aiki da kamfanin Mobil Oil Nigeria, kafin daga bisani ya zamo cikin jagororin kamfanin.

Ya fara shiga harkokin siyasa ne a shekarar 1992, lokacin da ya shiga jamiyyar Social Democratic Party (SDP) inda ya zamo mamba na ɗariƙar ‘Peoples Front’ wanda marigayi Shehu Musa Yar’Adua ke jagoranta, ɗarikar da ta ƙunshi manyan ‘yan siyasa irinsu marigayi Umaru Yar’Adua, Atiku Abubakar, Baba Gana Kingibe, Rabi’u Kwankwaso, Abdullahi Aliyu Sumaila, Magaji Abdullahi, Dapo Sarumi da Yomi Edu da dai sauransu.

An zaɓi Bola Tinubu a matsayin sanata mai wakiltar mazaɓar Legas ta yamma a jamhuriyya ta uku wadda ba ta yi nisan zango ba sojoji su ka yi juyin mulki tare da rushe mulkin dimokraɗiyya baki ɗaya.

Bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 June na shekarar 1993, sai Tinubu ya zamo ɗaya daga iyayen da su ka kafa gungun ƙungiyoyin rajin dawo da mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya ƙungiyar da ta shiga wayar da kan ‘yan ƙasa akan nuna rashin goyon bayan mulkin soja da kuma ayyana marigayi Moshood Abiola a matsayin wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa da aka soke na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Juyin mulkin da marigayi Shugaban ƙasa a wancan lokaci Abacha ya yi na zamowa shugaban ƙasa da kuma yunƙurin da ya yi na ɗaukar tsauraran matakai akan masu niyyar bashi matsala a mulkinsa, sai Tinubu ya ƙetare ya bar Nijeriya bai sake dawowa ba sai bayan rasuwar Abacha a shekarar 1998, inda aka fara kafa tubalin ginin jamhuriya ta huɗu.

A zaɓen shekarar 1999, Bola Tinubu ɗaya ne daga shuwagabannin jamiyyar Alliance for Democracy (AD), tare da su Abraham Adesanya da Ayo Adebanjo.

Ya shiga zaɓen firamare na jamiyyar ta AD a matsayin ɗan takarar ta na Gwamnan jihar Legas kuma ya samu nasara, inda ya doke abokan takararsa na lokacin Funsho Williams da Wahab Dosunmu, tsohon ministan ayyukan Nijeriya.

Don haka a zaɓen shekarar 1999, Bola Tinubu ya samu tsayawa takarar gwamnan jihar Legas a ƙarƙashin tutar jamiyyar AD, tare da samun nasarar lashe zaɓen cikin kwanciyar hankali.

A zaɓen shekarar 2015 kuwa, Tinubu shi ne jagoran gamin gambizar jam’iyyar AC, ANPP, da CPC waɗanda su ka dunƙule tare da komawa inuwar jamiyyar APC. Shi ne kuma ya jagoranci mara wa shugaba Buhari baya har ya samu tikitin takara a jami’yyar APC, har kuma daga bisani ya samu nasarar lashe zaɓen shugabancin ƙasar baki ɗaya.

Bola Ahmed Tinubu shahararran ɗan siyasane a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a ƙasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya baki daya.

Ana kallon Asiwaju a matsayin wanda ya daɗe yana jan zarensa tun daga dawowar Nijeriya kan mulkin dimokuraɗiyya a shekarar alif 1999.

A ranar 1 ga watan Maris 2023, Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da quri’a miliyan 8,794,726.

Tsohon matainmakinshugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ne ke biye masa da ƙuri’u miliyan 6,984,520. Sai kuma ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi wanda ya samu ƙuri’a miliyan 6,101,533. Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya zo na huɗu da ƙuri’u miliyan 1,496,687. Amma sai dai jam’iyyun adawa na PDP da LP sun ce ba za su karɓi sakamakon ba bisa zargin tafka maguɗi a mazaɓu da dama, inda kuma suka ce za su garzaya kotu.

Jama’a da dama na ganin Tinubu a matsayin uba a fagen siyasa sakamakon ƙarfin faɗa a ji da yake da shi a siyasar ƙasar Yarbawa da ma Nijeriya baki ɗaya.

Haka kuma ya kafa mutane da dama a Nijeriya inda ya yi musu hanya suka samu muƙamai a tarayya da jihohi.

A ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne Bola Tinubu ya zama Shugaban ƙasar Nijeriya na 16.