Sama da baƙin haure 70 sun ɓace a gaɓar ruwan Girka

Aƙalla mutane 78 ne suka mutu inda ake fargabar da dama sun ɓace, bayan da wani ƙaramin jirgin ruwa ɗauke da baƙin haure ya kife a ruwa a Ƙasar Girka, hatsari mafi muni da ya auku a wannan shekara, inji MƊD.

Kwale-kwalen wanda ya nutse a kudancin gaɓar tekun Girka, mai nisan kilomita 87 daga kudu maso yammacin Pylos, hukumomi sun ce masu aikin ceto sun fuskanci ƙalubale sakamakon kakkafar iska da ta kunno kai.

Yanzu haka dai kusan mutum 100 aka samu nasarar cetowa, inda ake ci gaba da laluben waɗanda suka ɓata.

An dai yi amfani da jirage masu saukar Angulu wajen ceto mutanen, kuma sojojin saman a ci gaba da lalube.

Tuni aka miqa mutum hudu daga cikin waɗanda aka ceto zuwa asibitin birnin Kalamata, sakamakon cewa jininsu ya sauka, wanda likitoci ke fargabar cewa rayuwarsu na cikin hatsari.

An dai miqa gomman waɗanda suke da lafiya zuwa sansanonin da aka ware musu, domin ba su kayayyakin sawa, kamar yadda MƊD ta tanadar musu.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan adadin mutanen da suka maƙale a ruwa, amma dai rahotanni na cewa adadin baqin hauren da suka fito daga ƙasashen Masar, Syria da kuma Pakistan ya haura 100.