An cafke tsohuwar shugabar makaranta da laifin yi wa ɗalibai fyafe

An samu wata tsohuwar shugabar makaranta, ‘yar asalin Isra’ila da laifin cin zarafin wasu ɗalibanta biyu a wata makarantar Yahudawa da ke Australia.

Kotu a birnin Melbourne na Australia ta samu Malka Leifer da laifin cin zarafin wasu yara mata guda biyu Dassi Erlich da Elly Sapper tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007.

Sai dai, ba a same ta da laifin yin lalata da yarinya ta uku da aka tuhume ta a kai ba, Nicole Meyer.

Leifer, mai shekara 56 ta musanta zarge-zargen da aka yi mata tun da farko, kuma ta kwashe shekaru tana ƙoƙarin ganin ba a mayar da ita Australia daga Isra’ila ba.

Sai dai a 2021 ne kotu ta ba da umurnin mayar da ita Australia ɗin daga Isra’ila.

Ɗaliban sun ce Leifer ta yi lalata da su a cikin aji, da kuma lokutan da suka kai ziyara gidanta daga makaranta.

Mai gabatar da ƙara Justin Lewis ya ce Leifer ta bayyana alamun cewa ita mai son bin mata ce.

Ya ce, ta yi amfani da matsayinta da kuma ƙuruciyar yaran da rashin saninsu game da abubuwan da suka shafi saduwa wajen ganin ta cimma nufinta.

Yaran a wancan lokacin ba su san komai game da lalata ba, saboda irin tarbiyyar da aka ba su, inda aka hore su kan tsarin rayuwa ta tsantsar bin addinin Yahudu, inji mai gabatar da ƙarar.

Ya ƙara da cewa, “kasancewar ta san an yi watsi da su a gida, sai ta nuna tamkar tana son su, kuma ta ce musu tana taimakon su ne.”

Sai dai lauyan wadda ake zargi, Ian Hill ya ce, zarge-zargen ba su da tushe.

Ayarin masu kare ta ɗin sun ce ba ta samu damar kare kanta yadda ya kamata ba, saboda tsawon lokaci bayan faruwar lamarin.

Leifer ta tsere zuwa Isra’ila bayan da aka tayar da maganar zarge-zargen.

Sai dai an kama ta a 2014 bayan da Australia ta buƙaci hakan, amma shekara biyu da ta wuce, sai wata kotun Isra’ila ta soke batun mayar da ita Australia, inda kotun ta ce tana da tavin hankali.

Amma masu bincike na farin kaya sun ɗauko hotunanta tana sayen kaya a kanti da kuma ajiye kuɗi a banki, abin da ya sanya Isra’ilar ta sake kama ta tare da gurfanar da ita a kotu cikin watan Fabrairun 2018.

Sannan bayan kwashe mako biyu ana sauraron ƙarar an samu Leifer da laifi 18 waɗanda suka jivanci cin zarafin Ms Erlich da Ms Sapper.

Za a yanke wa Leifer hukunci nan gaba kaɗan.