Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanku da jimirin karatun jaridarku ta Manhaja, mai farin jini. A wannan mako za mu tattauna ne a kan yadda kishin mata yake zarcewa daga kan kishin miji zuwa kishi a kan yaran da suka haifa.

Zan yi matashiya a kan wannan karin magana: “haushin kaza huce kan dami”. Wato yadda idon kishiyoyi yake rufewa ruf a kan kishi har ma su dinga ramuwa da fanshe haushin kishinsu a kan ‘ya’yan miji.

Haka ma wasu ‘yan mijin sukan ɗauki matar uba a matsayin kishiya wadda suke kishi da gasa da ita a kan duk wasu abubuwa na rayuwa.

Kalma ta kishi mun riga mun san cewa abinda take nufi shi ne sosuwar rai idan wani ko wata ya kusanci abinda kake ƙauna da sunan so.

Kishi dai halitta ce wacce Allah ya halicci kowanne ɗan Adam da ita. Wani zubin ma har da dabbobi ma suna yin kishi a kan abinda suke so. Amma a ɗabi’ar ɗan Adam mace ta fi zaƙewa wajen irin wannan baƙin kishi da ya wuce minsharrin.

Mace ta ɗauki namiji da tsananin daraja a kowanne vangare na rayuwarta, ta fi son ta mallake shi, shi kaɗai ba tare da ya haɗa ta da kowa ba. Kuma ba wai fa sai mijinta kaɗai ba. Ko wanene shi a rayuwarta sai ta yi kishi a kansa.

Tunda kowanne ɓangare na rayuwarta indai alaƙar namiji za ta gifta, to kuwa sai an samu mace ta ɗauki kishi. Ba a ce kar a yi kishi ba, amma ana yin kishin ya wuce makaɗi da rawa. Wani lokacin ma sai ya juye ya koma hassada da tsana.

Misali mace idan ta zama ƙanwar miji ko yayarsa, ko matar ɗan uwa, ko uwar miji, ko matar da, ko ‘yar miji ko kuma uwa-uba kishiya. To dole sai an yi kishi kawai saboda albarkacin wannan namijin da ya gifta a tsakani. Kuma kowacce so take ya zama nata, ita kaɗai ke iya sarrafa shi.

Duk a ture batun waɗancan alaƙoƙi, mu koma kan batun ‘ya’yan miji. Wato yaran kishiyarki. Mata saboda tsananin kishi a kan mazajenku da kuma tsanar da kuka yi wa kishiya sai a dinga huce takaicin kishin a kan yaran da ta haifa. Ke ma kuma yadda kika tsani ‘ya’yanta haka za ta tsani naki yaran. Tai ta yi musu mummunan fata da baki. To me ya yi zafi? Wannan shi ne Haushin kaza huce kan dami fa.

Ke wacce kika shigo kika samu mace da yaranta a gidan, da ma tun kafin ki shigo kin riga kin san cewa da ma yana da ‘ya’yan. Idan kin san ba za ki zauna da su ba, me ya sa za ki aure musu Uba? Sai ki jira ko za a dace ki samu mara aure wanda a kanki zai fara sanin daɗin haihuwa. Kinga sai ki ja zarenki shi ma kafin ya hango wata ya kawo gidan.

Sai kuma su waɗanda aka auro musu wata ta shigo ta samu ita ma nata yaran. Ke meye naki na kishi? Haushin kaza huce kan dami fa kenan. Ko uwarsu ba wanda ya ce ki tsane ta don tana kishiyarki balle abinda ta haifa. A musulunce fa musulmi ɗan uwan musulmi ne. Kuma Annabi ya hore mu da so wa ɗan uwa abinda kake so wa kanka.

Kuma shi ɗan da aka haifa ba ya nan a Duniya lokacin da aka yi auren da ke kike gani an vata miki. Ba shi da wani laifi sai don huce haushin uwarsa a kansa. Shi fa ba shi ya zaɓi a haife shi a wannan fitinannen gida naku ba. To meye nasa?

Don haka mata su sanitsanar wannan ɗan kishiya ya tashi daga kishi ya zama hauka da hassada da kuma zalunci. Domin bai kashe miki kowa ba, bai ci miki komai ba.

Sai ka ga kishiyoyi a gida kullum kowacce ba ta ƙaunar ɗan wata. Ga faɗa da hassada ko yaya uban ya nuna kulawarsa ga ɗan da ba naki ba, sai ki nuna haushi da hassada a kan haka. Saboda ke kin fi son a kula naki ke kaɗai.

Amma wani lokacin yaran sukan ba da iyayensu. Sai ku yi faɗanku ku gama, kuma jini ba qarya ba ne. Dole yaran za su so junansu. Kuma idan da rabo ma, su girma su yi zumunci kuna raye.

Amma wani lokacin iyaye maza suna ba da tasu gudunmowar a kan haka. Domin su iyaye maza su ne shugabanni. Kuma kowa na gidan su ne suka kawo shi fa. To nuna wariyar na meye kuma? Dukkansu yaranka ne na cikinka. Kuma a cikinsu ba ka san wa Allah zai yi wa arziki ya tallafa maka ba.

Ya kai Maigida ka sani, an sha yin irin haka a tarihi. A ga matar da ka wulaƙanta ka ƙasƙantar da ita a gidanka kuma idan tsufa ya zo maka ka ga ita da zuri’arta su za su tallafe ka.

Maza wataƙila suna mantawa ne akwai ranar ƙin dillanci. Wato lokacin da tsufa ya cim musu kuma ƙarfinsu ya ƙare. Ba su da ma lafiyar fita su nema. A lokacin idan ba su da yaran da suka kawo ƙarfi, kuma masu imani, to za su wahala.

To ai gara ka fara yi wa gobenka tanadi tun a yau. Babu wani abu da zai ragu tare da kai don ka daidaita yaranka da matanka ba tare da wariya ba. Sai ma lada da za ka samu na bin umarnin Allah.

Sannan kuma ka sani, idan yaranka suka tashi kana wariya tsakaninsu, za su tsani juna. Su ƙi yin zumunci ko bayan ranka zuriyyarka za ta kasance a tarwatse.

Haka idan yaro uwarsa ta fice ta bar shi. Ko kuma ta mutu ta bar shi, shi ma yana ganin garari a Duniyar nan. Idan kishin ne ma, ai ta fita ta bar miki gidan ko ma Duniyar gabaɗaya ko? Kuma ke ma ba ki san taki ƙaddarar ba. Ba ki da tabbacin cewa ke ma za ki taso tare da naki yaran. Kuma inda ta je lahira ba gaggawa ta yi ba, ke ma za ki je ne. Wataƙila ma kin kusa tafiya ke ma ba ki sani ba.

Sai ka ga irin wannan kishiyar na kaucewa, za a koma huce kishin kan yaran da ta tafi ta bari. Wata har kisan kai take yi ko ta illata ɗan miji duk saboda kina jin haushin uwarsa. Don Allah ‘yaruwa ina tauhidinki da imaninki suka tafi?

Shi ma uban ba abinda ya shafe shi. Daga ɗa ya rasa uwa a gida, shikenan har uban ma sai ya rasa shi gabaɗaya. Don rashin tsoron Allah na wasu mazan.

Amma akwai mazaje masu kulawa, sai dai ba su da lokacin da za su sa ido a kan gidansu, saboda yanayin sana’arsu. Ko kuma suna tafiye- tafiye, ba sa zama a gari. Sai su damqa yaran amana gurin matar gidan ita kuma idan ba mai tsoron Allah ba ce sai yadda ta ga dama.

Wasu kuma suna ƙorafin cewa uwar yaran ce mara kirki kuma ta zalunce ki lokacin kuna tare. Amma wannan ba ita ba ce. Ya kamata a gane banbancin da kyau. Kishiya daban, ɗanta daban. Idan ba ki kula da amanar ‘ya’yanta ba, duk da mugun halinta gare ki, ba ruwan Allah. Kuma za ki samu zunubi mai yawan gaske.

Haka idan su ma yaran mijin ba sa kyautata miki ko sunamunafuntarki, ai Allah yana gani. Kuma zai yi hisabi a tsakaninku. Amma idan kika cuce su, Allah yana kallonki. Ke dai ki ji tsoronsa shi kaɗai.

Haka wani kina iya ƙoƙarinki uban ba ya gani. An san zuciya ba ta da ƙashi. Amma ki daure ki zauna da su, da ma kowa tsakaninki da Allah. Duk wanda ya cuce ki, kika yi haquri komai zai wuce kuma za ki samu rabo mai yawa.

Kuma ki lura, shi fa yaro komai kika yi masa yana cikin ƙwaƙwalwarsa ba ya mantawa. Sai ki yi ta taka-tsan-tsan.

Ki sani, a rayuwar nan sai ki ga ba ki mori naki yaran ba, ko kuma su Allah bai musu arziki sosai ba. Sai ki ga yaran riƙon nan kin ji daɗi a hannunsu. Sun zamar miki tamkar na cikinki. Har ma su tallafa wa yaranki idan ba su da ƙarfi.

Sannan ki toshe kunnenki a kan zuga. Mutane za su yi zuwar miki da nau’oin zugar su. Kowa da abinda zai ce. Don kawai suna son su tarwatsa miki farin ciki. Kuma idan kin bibiya ba masoyanki na kirki ba ne.

Kuma ki sani, shi mijin nan naki kin aure shi ne don soyayyar da take tsakaninku. Kuma abinda ya dace ki yi shi ne, in dai har son gaskiya kike masa na tsakani da Allah, ai ya kamata ki so duk wani wanda yake jingine da shi.

In dai son Allah ne da Annabi, ba shi zalla za ki so ba. Dole ki so iyayensa, ‘yanuwansa, danginsa, da sauransu. Haka har mata ko matansa idan yana da su, da ‘ya’ya. Ko ba ki so su ba, ya kamata a ce sun aminta daga dukkan wani sharrinki. Ma’ana, kada su zama abun cutarwarki.

Kuma sannan Hausawa sun ce: “ma so uwa ya so ɗanta”. Don haka sai a kula. Allah ya datar da mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *