Rashin lafiya zata yi sanadin sakin wanda ake zargi da kisan kiyashi a Rwanda

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta ce Felicien Kabuga, da ke fuskantar tuhuma bisa zargin yana da hannu a kisan kiyashin Rwanda cewa ba shi da isasshiyar lafiyar da zai fuskanci tuhuma.

Kotun ta ce za ta yi amfani da wata dokar wacce za ta yi kamanceceniya da shari’ar da ake wa Kabuga mai shekaru 80, amma ba za ta yanke masa hukunci ba.

Alƙalai a kotun da ke Hague sun ce Kabuga, wanda ake ce-ce-ku-ce kan takamaiman ranar haihuwarsa, da wuya ya sake samun isasshiyar lafiya a nan gaba.

An yanke shawarar ne bayan likitoci sun gano cewa Kabuga na fama da cutar mantuwa. Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da zai faru da Kabuga wanda ke tsare a gidan yarin kotun ba.

An kama Kabuga a Faransa a shekarar 2020 bayan fiye da shekaru 20 yana tserewa.

A watan Satumban bara ne dai aka gurfanar da shi gaban kuliya, inda masu gabatar da kara suka zarge shi da kafa kafafan yaɗa labarai na nuna ƙyama, waxanda suka buƙaci ƙabilar Hutu da su kashe ‘yan ƙabilar Tutsi da ke adawa da juna, tare da bai wa mutane makamai.

Masu gabatar da ƙara sun ce Kabuga ya tallata kalaman nuna ƙiyayya ta shirye-shiryensa, a gidajen Rediyon da Talibijin na Libre des Milles Collines, da kuma ba wa mayaƙan ƙabilar Hutu makamai.

Yana da wuya a gurfanar da waɗanda ake tuhuma a gaban kotunan duniya da matsalar da ta shafi ƙwaƙwalwa.

Kabuga na ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da kisan kare dangi a Rwanda na ƙarshe da suka fuskanci shari’a, inda kotun ta yanke wa mutane 62 hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *