Za a sanar da jadawalin Firimiya na 2023/24 a makon gobe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Za a bayyana jadawalin Firimiya na gasar 2023/23 a ranar Alhamis, 15 ga watan Yunin 2023.

Lokacin ne za a fayyace ranakun da za a buga dukkan karawa 380 da lokutan da za a yi wasannin.

Za a fara kakar Firimiya ta 2023/24 ranar Asabar 12 ga watan Agustan 2023 – za kuma a yi wasannin ƙarshe ranar Lahadi 19 ga watan Mayun 2024.

Wannan ce kakar farko da za a fara ba tare da cin karo da tsaiko ba, bayan da cutar Korona ta haifar da koma-baya na kaka biyu.

Sannan a kakar nan gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatar, wadda Argentina ta lashe a 2022, ta sa aka dakatar da wasannin ana tsaka da gasar.

A wannan kakar babu ƙungiyar da za ta yi wasa biyu a lokacin hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Idan aka fara kakar bana ranar Asabar 12 ga watan Agusta, zai zama kwana 76 ke nan tsakani da aka kammala kakar da ta wuce ta 2022/23.

Manchester City ce ta lashe Firimiya na 2022/23 na uku a jere kuma na biyar a kaka shida.

Waɗanda za su wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai a 2023/24 sun haɗa da City da Arsenal da Manchester United da Newcastle, wadanda za su buga gasar Zakarun Turai.