An kama mutum 2000 kan tada tarzoma a Faransa

Rahotanni daga ƙasar Faransa sun ce, sama da mutane dubu biyu ne aka kama a Faransa, tun bayan tarzomar da ta biyo bayan kisan da ‘yan sanda suka yi wa matashi Nahel.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Ƙasar ce ta bayyana haka a ranar Lahadi.

Zanga-zangar wadda aka shafe kimanin kwana biyar ana gudanar da ita, hukumomin Faransa sun tabbatar da kama mutane 719 a ranar Asabar.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa ana samun raguwar tarzomar da aka faro tun a ranar Talatar da ta gabata.

Ministan Kulada Harkokin Cikin Gida na Faransa, Gerald Darmanin, ya sanar a ranar Asabar cewa an tura jami’an ‘yan sanda kimanin 45,000 zuwa sassan ƙasar don kwantar da tarzomar.