‘Yan bindiga sun kashe fasto a Ogun

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga sun kai hari a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ke Jihar Ogun inda suka kashe fasto kana suka yi garkuwa da wasu mambobin mujami’ar da ke tsaka da ibada.

Majiyarmu ta ce harin ya auku ne a wannan ƙarshen makon a Abule-Ori da ke yankin Ƙaramar Hukumar Obafemi Owode a jihar.

Kwamandan rundunar tsaron jihar, Soji Ganzallo, shi ne ya tabbatar da faruwan hakan ga manema labarai da safiyar Lahadi.

Kwamandan ya ce jami’ansu sun kuɓutar da mambobin cocin bakwai da aka yi garkuwa da su tare da kashe mutum guda daga maharan.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na rundunar, Moruf Yusuf Ganzallo, ya rattaɓa hannu ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12am a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce an kai gawar ɗan bindigar da aka kashe ɗakin ajiyar gawa da ke kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *