Shugaban Guinea-Bissau ya ziyarci Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo, a Legas.

Embalo, wanda jigo ne a ƙungiyar ECOWAS, ya ziyarci Tinubun ne a ranar Asabar.

Shugaba Tinubu ya yi hutun sallah ne a Legas tun bayan da ya dawo daga London a ranar Talata.

Embalo ya zama Shugaban Ƙasa a Afirka na farko da ya ziyarci Tinubu tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Nijeriya na 16 a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *