Kasashen Waje

Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Daga WAKILIN MU 'Yan jam'iyyar National League for Democracy a ƙasar Myanmar, sun yi kira da a sako Aung San Suu Kyi tare da sauran jagororinsu da aka tsare a Talatar da ta gabata. Suna masu bayyana juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi a ƙasar a matsayin al'amari da ya yi wa tarihin sojin ƙasar tabo mara kyau. Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata sojoji suka kama Suu Kyi da ta kasance shugabar jam'iyyarsu tare da shugaban ƙasar, Win Myint. Bayan juyin mulkin, ba tare da ɓata lokaci ba sojojin suka naɗa wani tsohon janar, Min Aung Hlaing,…
Read More
China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

Daga FATUHU MUSTAPHA Kasar China ta sanar da ɗaukar matakin haramta wa ɗalibai 'yan firame da na sakandare yin amfani da wayoyin salula a cikin aji. China ta ce, ta ɗauki wannan mataki ne domin kare ɗaliban daga fitinar intanet da kuma 'TV game' da kan hana ɗalibai maida hankali kan karatu yadda ya kamata. A wata takardar sanarwa da Ma'aikatar Ilimin ƙasar ta raba wa makarantu a Litinin da ta gabata, ma'aikatar ta ce daga yanzu ba a yarda ɗlibai a makarantun firamare da sakandare su riƙa amfani da wayoyi a aji ba. Tana mai cewa, "Duk ɗalibin da…
Read More
China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

Daga WAKILIN MU Rahotanni daga ƙasar China sun nuna hukumomin ƙasar sun cafke wasu mutum 80 bisa zarginsu da harkar haɗa jabun maganin allurar rigakafin cutar korona. Wani kamfanin dillancin labarai na ƙasar, Xinhua ya ruwaito cewa, ana zargin tun a watan Satumban da ya gabata waɗanda lamarin ya shafa suka soma harkar haɗa jabun rigakafin korona tare da sayar wa mutane da sunan magani mai inganci. Hukumomin ƙasar sun ce, jabun rigakafin korona guda 3000 suka kama waɗanda aka yi aikin haɗawa a sassa daba-daban a ƙasar. Kafin wannan lokaci, China ta samar da allurar rigakafin cutar korona da…
Read More
An yanke wa dan Turkiyya shekaru 1,075 a kurkuku

An yanke wa dan Turkiyya shekaru 1,075 a kurkuku

Daga Umar Mohammed Gombe Wata Kotu a Istanbul na kasar  Turkiyya ta daure shugaban wata kungiyar asiri mai suna Adnan Oktar shekaru sama da 1,000 a bisa samun sa da aikata wasu laifuka 10, a cewar wata majiyar shari’a a kasar. An kama Adnan Oktar mai shekaru 64 ne a shekarar 2018, a wani samame da jami’an tsaron kasar suka kai a daidai lokacin da suke tsaka da miyagun laifuka, inda aka kama da yawa daga mabiyan sa wadanda yawancin su mata ne. Ana tsare da shi tun watan Yunin 2018 a matsayin wani bangare na fatattakar kungiyar sa da…
Read More
Kotun Kolin Amurka ta tabbatar wa Biden nasarar zabe

Kotun Kolin Amurka ta tabbatar wa Biden nasarar zabe

Daga Umar M. Gombe Kotun Koli na Amurka ta kawo karshen dogon takaddamar da ya dauki lokaci ana yi game da zaben shugaban kasa a kasar tun a watan Nuwamba, inda ta tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na Democrat Joe Biden nasara. A cikin hukuncin da ta yi ba ranar Juma'a, kotun kolin ta kori karar da Shugaba Donald Trump ya shigar game da zargin tafka magudin zabe da aka yi a Pennsylvania da kuma jihohi uku na kasar. Jihohin hudun sun gabatar da shaidu gaban kotun, inda kuma suka bukaci alkalan kotun da su yi watsi da karar,…
Read More