Kotun Kolin Amurka ta tabbatar wa Biden nasarar zabe

Daga Umar M. Gombe

Kotun Koli na Amurka ta kawo karshen dogon takaddamar da ya dauki lokaci ana yi game da zaben shugaban kasa a kasar tun a watan Nuwamba, inda ta tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na Democrat Joe Biden nasara.

A cikin hukuncin da ta yi ba ranar Juma’a, kotun kolin ta kori karar da Shugaba Donald Trump ya shigar game da zargin tafka magudin zabe da aka yi a Pennsylvania da kuma jihohi uku na kasar.

Jihohin hudun sun gabatar da shaidu gaban kotun, inda kuma suka bukaci alkalan kotun da su yi watsi da karar, wadda suka ce ba ta da hurumin doka a kudin tsarin mulkin kasar ko kadan.

Inda a karshe kotun da tabbatar da nasarar zaben ga Mista Joe Biden, bayan lashe mafi yawan kwalejojin zaben kasar, wadda tuna har ya fara shirye-shiryen karbar mulki a watan 1 na shekarar da za a shiga tare da nade-naden mukaman gwamnatin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *