El-Rufa’i ya sake killace kan sa bayan bullar cutar korona a gidan sa

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

Sakamakon samun wasu daga cikin manyan ma’aikatan gwamnatin Jihar Kaduna da kuma mutum biyar daga cikin iyalin sa da kamuwa da cutar korona, Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya sake killace kan sa har sa har sai an yi masa gwaji.

Gwamnan ya bayyana haka ne a daren Juma’a a cikin wani bidiyo mai tsawon minti 1:15.

Wannan shi ne karo na biyu da ya killace kan sa bayan tabbatar da ci-gaba da hauhawar kamuwa da cutar a Jihar Kaduna da sauran jihohin Nijeriya.

A bidiyon, gwamnan ya ce, “Ana ta ci gaba da kamuwa da cutar, har gwaji ma ya nuna wadansu manyan ma’aikatan gwamnatin Jihar Kaduna da kuma mutum biyar daga cikin iyali na sun kamu da cutar.

“Yanzu haka na sake killace kai na har sai an sake yi min gwaji zuwa ranar Lahadi.”

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Jihar kan su ci gaba da kiyaye dukkan matakan da masana lafiya su ka bayyana kamar yawan wanke hannu, bayar da tazara, kauce wa cinkoson mutane da kuma sanya takunkumi ko da yaushe don kauce wa yaduwar cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *