Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisa ga Maryam Sanda

Daga Umar Mohammed Gombe

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi.

A wani zama da kotun ta yi na mutum uku karkashin jagorancin Jastis Stephen Adah, a yau Juma’a da yamma, akan hukuncin da ta yanke, ya yi watsi da daukaka karar da Maryam Sanda ta shigar gaban kotun bisa rashin cancanta.

A farkon wannan shekarar idan za a tuna, Mai Shari’a Yusuf Halliru na Babbar Kotu a Abuja da ke Maitama, ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, lamarin da ya sa ta daukaka kara don kalubalantar hukuncin.

Tun da farko dai gwamnatin tarayya ce ta gurfanar da Maryam Sanda da wasu mutum uku a kan laifuka uku da suka hada da kisan kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *