Daga ABBA MUHAMMAD
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin sa da nasarar da dan damben Nijeriya, Anthony Joshua, ya samu a kan Kubrat Pulev a fafatawar da suka yi a daren jiya Asabar.
A sanarwar da ya fitar ta hannun kakakin sa, Femi Adesina, Buhari ya ce Joshua ya bai wa masoya dambe a duniya da ma Nijeriya farin ciki sosai.
Shugaban ya ce ya tuna da haduwar da ya yi da Joshua a Ingila, inda ya bayyana shi a matsayin mai saukin kai kuma wanda ya samu tarbiyya, ya ce zai yi nasara sosai a rayuwar sa.
Ya kuma yi wa dan damben fatan nasara a fadan sa na gaba, inda ya ce ‘yan Nijeriya za su taya shi da addu’a.