Juyin Mulkin Nijar: Sai bayan shekara uku za mu miƙa mulki ga farar hula – Tchiani

Daga BASHIR ISAH

Jagoran juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya bayyana cewa sai bayan shekara uku sojoji za su miƙa mulki ga farar hula a ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a jawabin kai-tsaye da ya yi wa ‘yan ƙasar a talabijin ranar Asabar da daddare.

Jawabin nasa na zuwa ne bayan tattaunawar da suka yi da tawagar ECOWAS ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya).

Janar Tchiani ya ce a tsakanin wata ɗaya mulkin sojin zai kafa kwamitin da zai samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ya ƙara da cewa, duk da dai Nijar ba ta fatan faɗawa yaƙi, amma za ta kare kanta idan buƙatar hakan ta taso. Tare da cewa har yanzu ƙofar sulhu a buɗe take.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ECOWAS ba ta maida martani kan jawabin da Tchiani ya yi ba. Kuma ana sa ran Abdulsalami ya ba da bayanin sakamakon tattaunawar da suka yi.

Wannan shi ne karo na biyu da ECOWAS ke tura tawagarta ƙasar Nijar ɗin don tattauna yadda za a maido da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.