Matasan Nijeriya, kada ku karaya!

Kwanan nan, ƙasashen duniya sun yi bikin murnar ranar matasan duniya. Ranar 12 ga watan Agusta ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar matasa ta duniya a shekarar 1999, kuma ita ce bikin shekara-shekara na rawar da matasa maza da mata ke takawa a cikin al’umma. Yana ba da damar wayar da kan jama’a game da ƙalubale da matsalolin da ke fuskantar matasan duniya

Kowace shekara, Ranar Matasa ta Duniya ta kasance wani jigo na musamman wanda ke magance matsalolin ƙalubale da matasa ke fuskanta. Taken ranar matasa ta duniya a shekarar 2023 shi ne ‘Green Skills for Youth: Towards a Sustainable World.’ A nan Nijeriya, an gudanar da taron ne da jawabai da kuma al’amuran mutane da ƙungiyoyi daban-daban, waɗanda suka shafi vangaren matasa na al’umma.

A cikin saƙon nasa, Shugaba Nijeriya Bola Tinubu ya jinjina wa matasan Nijeriya saboda ƙwazon da suke da shi, da basirar ƙirƙire-ƙirƙire da kuma damar da ba ta da iyaka. Ya kuma tabbatar wa da matasan cewa ɗaukacin al’ummar ƙasar nan na da burin ganin cewa matasan sun samu damarmaki.

Ya amince da ƙaruwar tasirin da ɗimbin matasan Nijeriya ke da shi a fannonin da suka shafi fasaha a faɗin duniya, ya kuma sha alwashin cika alƙawarin da ya ɗauka na samar da sabbin ayyukan yi miliyan ɗaya a fannin tattalin arziki na zamani domin su ƙara ba da gudujmawa ga cigaban tattalin arzikin ƙasa.

Kuma a bisa taken bikin ranar matasa ta duniya ta bana, shugaban ya jaddada buƙatar matasa su shiga cikin ajandar gwamnatinsa na faɗaɗa guraben ayyukan yi da bayar da shawarwarin samar da hanyoyin ayyuka a matsayin wani muhimmin ɓangare na hada-hadar cigaba a Nijeriya a halin yanzu da nan gaba.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban aasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ƙarfafa wa matasan Nijeriya gwiwa da su ci gaba da kasancewa masu kyakykyawan fata da fatan ganin sabuwar Nijeriya, wadda a cewarsa, za ta kasance a kan cigaban matasa da samar da ayyukan yi.

A yayin da duniya ke bikin zagayowar ranar matasa na shekara-shekara, matasan Nijeriya na cikin tashin hankali a ƙasarsu. Suna fuskantar ƙalubale da yawa masu ban tsoro a yau waxanda ke kawo cikas ga makomarsu kuma suna barazanar hana cikar burinsu, babu shakka. Na farko, tsarin zamantakewa da na ilimi sun bar su da kasa shirya su don ƙalubalen duniya ta zamani. Rahotanni sun bayyana cewa, sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a faɗin Nijeriya, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ya ƙaru daga miliyan 10.5 shekaru 10 da suka gabata zuwa kimanin miliyan 20 a yau, inda kusan kashi 30 cikin 100 na matasan Nijeriya ba su da ilimi na karatun sakandare.

Tare da wannan yawan rashin aikin yi na matasa, inda fiye da rabin al’ummar ƙasar ba su da aikin yi, al’ummar ƙasar za su cigaba da tavarvarewa a cikin matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da tsaro.

Wannan rashin cigaban tattalin arziki na matasa ya riga ya bayyana a faɗin Nijeriya, ta hanyar hare-haren Boko Haram, fashi da makami, garkuwa da mutane, ƙungiyoyin asiri, fataucin miyagun ƙwayoyi da cin zarafi, zamba, kisan kai da tashin hankali na ‘yan aware.

Sannan kuma akwai magudanar hankali inda matasan Nijeriya ke ƙaura zuwa wasu qasashe domin neman ayyuka. Suna tserewa daga ƙasar ta kowace hanya da za su iya, inda wasu ke yin kasada da rayukansu a matsayin miyagu ko kuma bi ta Arewacin Afirka inda da yawa ke halaka ko dai a cikin sahara ko kuma nutsewa cikin kwale-kwalen da ke ƙoƙarin tsallakawa Turai.

A matsayinmu na jarida, muna yin Allah wadai da yadda gwamnatocin da suka shuɗe suka yi wa ƙasar nan ba daidai ba, ta yadda mafi yawan matasanmu ba za su iya rayuwa mai inganci ta hanyar aiki na gaskiya ba. Muna yin Allah wadai da baqin zuciyar da wasu ’yan siyasa suke ganin matasa a matsayin mutane masu rauni da za a yi amfani da su a matsayin ’yan daba da ’yan iska wajen yi wa ’yan ƙasarsu ɓarna.

Duk da haka, muna godiya da jinjinawa da yawa daga cikin matasanmu da suka tashi tsaye wajen ganin su cika burinsu na rayuwa don zama masu cin nasara a duniya a fagen wasanni, kiɗa da nishaɗi, fasaha, masana’antu da ilimi. Waɗannan suna daga cikin kyawawan misalan da ya kamata matasan al’ummar ƙasar nan su lura da su, kada su karaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *