Yaƙin Iran: Da yiwar Turkiyya ko Pakistan ta karɓi baƙuncin tattaunawar tsagaita wuta

Spread the love

Wani babban jami’in Iran ya bayyana cewa ƙasar Pakistan ta isar da wata muhimmiyar shawara daga Amurka zuwa Iran, inda ake duba yiwuwar gudanar da tattaunawa a ƙasar Pakistan ko kuma Turkiyya domin rage zafin rikicin da ke ci gaba da addabar yankin Tekun Gulf.

Jami’in, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa wannan mataki na daga cikin alamun farko da ke nuna yiwuwar Iran ta fara la’akari da hanyoyin diflomasiyya, duk da cewa a fili gwamnatin Tehran tana ci gaba da musanta cewa akwai wata tattaunawa da ke gudana da Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta aika da wani tsarin sharuɗɗa mai ƙunshe da matakai 15 ga Iran, wanda ya haɗa da:

Kawar da ajiyar uranium mai matuƙar hadari, dakatar da aikin inganta sinadarin nukiliya, takaita shirinta na makamai masu linzami, dakatar da tallafawa ƙungiyoyin kawance a yankin.

Sai dai majiyoyi daga gwamnatin Isra’ila sun nuna shakku kan yiwuwar Iran ta amince da irin waɗannan sharuɗɗa, tare da fargabar cewa Amurka na iya sassauta wasu ƙa’idoji yayin tattaunawa.

A gefe guda kuma, kasuwannin duniya sun nuna sauki bayan ɓullar labarin wannan shiri, inda farashin mai ya sauka, yayin da hannayen jari suka fara farfaɗowa sakamakon fatan kawo ƙarshen yaƙin da ya ɗauki kusan makonni huɗu.

By ukarofi