Yaƙin Iran: Kasashen Asiya sun koma salon lokacin Korona 

Spread the love

Kasashen Asiya na fuskantar matsanancin ƙarancin mai sakamakon rikicin Iran, wanda ya kusa rufe mashigar Hormuz, wato wata hanya da kusan kashi 20% na man duniya ke bi.

ƙasashe da dama na duba hanyoyin da suka yi amfani da su a lokacin annobar Korona, ciki har da; aiki daga gida, rage zirga-zirga, rage amfani da makamashi.

Koriya ta Kudu na la’akari da dawo da tsarin aiki daga gida, yayin da Philippines ta rage kwanakin aiki a wasu hukumomi.

Wasu ƙasashe sun ɗauki matakai masu tsauri:

Pakistan ta rufe makarantu na wucin gadi.

Sri Lanka ta ware rana guda a mako a matsayin hutun ƙasa.

Singapore ta ƙarfafa amfani da kayan da ke rage cin wuta.

Japan na shirin kashe biliyoyin kuɗi domin rage farashin mai, yayin da New Zealand ke bai wa talakawa tallafi kai tsaye.

By ukarofi