Tun 7 ga wata rayuka na cigaba da salwanta a Gaza

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ba wani babban labari a duniya yanzu da ya sha gaban halin da a ke ciki a yankin Gaza na Falastinawa inda jiragen yaƙin Isra’ila ke cigaba da ruwan boma-bomai kan gine-gine da nuna zummar murƙushe ’yan bindigar HAMAS. Tabbas duk yadda za a iya auna masu rike da bindiga to la shakka sai an tava waɗanda ba ko allura a hannun su.

Wani abun damuwa ma shi ne taba ran mata da yara. Bincike ma na nuna hatta jarirai ma ba su tsira ba. Kuma a gaskiya ba a san ranar da yaƙin ko hare-haren nan za su tsaya ba. Hotunan da gidajen talabijin ɗin duniya ke nunawa kan nuna yadda dogayen benaye ke zubewa kamar an narkar da su saboda nauyin boma-boman da sojan Isra’ila ke saukewa. Yo shi dogon gini in rugujewa ma ya yi don rashin inganci sai ya danne mutane kuma zai yi wuya a rasa samun waɗanda za su rasa ran su.

Fada ne tsakanin mai jefa roka da ba lalle ta isa inda a ka auna ta ba da rundunar da ke mallakar makaman ƙare dangi. Haka kawai ma Isra’ila na da tsauri in an duba yandda kwanakin baya a ka tabbatar sojojin ta sun bindige wata ’yar jarida Shireen Abu Akleh da ke aiki da gidan talabijin na Aljazeera don ba mamaki yadda ta kan ɗauko rahotanni daga yankunan da Isra’ila ta mamaye ta na ɗanɗanawa Falasɗinawa azaba.

Duk wanda Isra’ila ta kashe jinin sa kan tafi hakanan sai dai ’yan uwan sa su yi ta jimami. Wato babbar damuwar ita ce yadda Isra’ila ke da goyon baya na fitar hankali daga manyan qasashen duniya da ya dace su zama a tsakiya wajen adalci don sasanta wannan fitina da ta gagara warwarewa fiye da shekaru 70.

Mai ɗaki shi ya san inda ya ke yi ma sa yoyo wato ma’ana duk yadda mutum da ke nesa da Falasdinawa ya ke fassara lamuran su ba zai kai su jin takaici ko damuwa ga halin da su ke ciki ba. Yara kan iya tashi tun ba sa fahimtar komai cikin tashin hankali na rashin tabbacin kare rayuwar su. Wasu kuma tun su na matasa su kan tsinci kan a gidajen yarin Isra’ila in sun yi sa’a bayan sun yi farin gashi a sako su.

Wato gaskiyar magana yankin na Falasɗinawa ba shi da wani katabus a hukumance don Isra’ila ce kan yi uwa da makarbiya kan duk abun da Falasɗinawa ke samu daga helkwatar gwamnatin su da ke birnin Ramallah. Isra’ila kan zaɓi ƙin yin aiki da duk wata yarjejeniya ta neman kawo ƙarshen fitinar nan don shiga zaɓi mafi sauki na amincewa da kafa ƙasar Falasdinawa a gefe da Isra’ila.

Ma’ana Falasɗinawa za su yi murna su sadaukar da fiye da rabin ƙasar su ga Isra’ila matuƙar za a bar mu su sauran ƙasar da ta rage don kafa ƙasar su mai helkwata a gabashin birnin Kudus. Ba zaman da ya fi daɗi irin na ’yanci ko da ba sulalla ba a aljihu. Tsuntsu a kan reshen bishiya a daji ya fi walwala
da tsalle-tsalle fiye da ya zama ya na cikin keji da ruwa da a ka surka ma sa suga.

Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya Abdullah Shawesh ya ce cikin waɗanda ke gwagwarmayar kwatowa Falasɗinawan haƙƙin su akwai mabiya addinin Kirista da ma Yahudawa.

Jakadan ya ce duk mai tausayi a zuciyar sa zai marawa muradin Falasɗinawan na samun ƙasar kan su daga mamayar Isra’ila.

“Daga 7 ga watan nan adadin waɗanda su ka mutu a Gaza sun kai 5,791 inda ciki ma akwai yara 2,360, mata 1,421 da kuma tsoffi 217.” Inji Jakada Shawesh a taron manema labaru a ofishin jakadancin Falasɗinu a Abuja.

“Falasɗinawa 16,297 sun samu raunuka daban-daban inda fiye da 1000 ke ƙarƙashin ruguzazzun gine-gine da a ke ta fama ceto su.”

Shawesh ya zayyana gwagwarmayar da su ke yi ta neman kwatar ‘yanci ce ba faɗan addini ba ne kamar yanda ya ce musamman wasu mabiya addinin kirista a Nijeriya ke ɗaukar Falasɗinawa a matsayin su na Larabawa duk Musulmi ne alhali su na da mabiya addinin Kirista don cikin hare-haren Isra’ila ma ta ruguza wata tsohuwar majami’a mai tarihi a Gaza.

Shawesh ya ƙara da cewa, kamar yadda ƙasashen Afurka su ka yi gwagwarmayar samun ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka, hakanan Falasɗinawa ke yunƙurin samun ‘yanci da ya ce sun rasa tun 1948.

Jakadan ya ce duk kayan agajin da a ke shigowa da shi Gaza daga mashigar Rafa ta Masar ba su fi biyan buƙatar kashi 3% na jama’ar Gaza ba.

Shawesh ya ce Nijeriya na da gagarumar gudunmawar da za ta bayar wajen ciccibar neman ‘yancin Falasɗinawa ya na mai godewa ‘yan Nijeriya da irin goyon bayan da su ke ba wa ƙasar sa.

Da a ka tambaye shi ko Hamas ba ‘yan bindiga ne masu sava doka da oda ba?

Jakadan ya ce, gasawa Falasɗinawa aya a hannu ya kawo kafuwar Hamas a 1987 inda ba qungiyar gabanin nan tun mamaye yankin Falasɗinawa.

Sakataren Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen Arewa ta tsakiya Pastor Simon AS Dolly ya ce nuna tsana ga Falasɗinawa don bambancin addini ba daidai ba ne.

Haƙiƙa tatatunawa da ma muhawara mai zafi kan halin da a ke ciki a Gaza na daga manyan darussa da ‘yan Nijeriya ke wuni su tashi da shi inda wasu ra’ayin su kan zo iri ɗaya wasu kuma su yi harshen damo.

Gaza: Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa ba ƙasar da ta fi ƙarfin dokokin duniya:

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ba wata kasa da ta fi ƙarfin dokokin duniya kuma ‘yan Hamas ba su kai hari haka kawai ba wani dalili ba ko takura ba.

Guterres na magana ne a gaban muhimjmin taron kwamitin tsaro na majalisar da ya fi kowane kwamiti tasiri a duniya.

Duk da Guterres ya nuna ba daidai ne harin da Falasɗinawan Hamas su ka kai kan Isra’ila a ranar 7 ga watan nan ba, amma kuma ba daidai ba ne har ila yau a yi mu su kuɗin goro wajen horo ba. Duk da hakan ne kai tsaye Guterres bai ambaci sunan Isra’ila ba amma ya zaiyana karara cewa an take dokokin duniya a faɗan da a ke yi ko hare-haren jiragen saman yaƙi kan Gaza.

Hakanan Guterres ya ce shekaru 56 Falasɗinawa su ka yi a cikin uƙubar mamaye mu su ƙasa.

Guterres wanda ya zaga da kan sa ya duba yanda a ke turo kayan agaji daga cikin Masar zuwa Gaza ya yaba da halin jinƙai da a ka samu nasara ɗauka.

Wannan jawabi na Guterres ya husata Isra’ila ainun inda har ta kai ga ministan harkokin wajen Isra’ila Eli Cohen ya nuna yatsa ga Guterres ɗin ya na mai cewa ko dai ba a duniyar da mu ke ciki ya ke rayuwa ba, wato ma’ana ko bai ga mutanen da ‘yan Hamas su ka kashe ba ne a cikin Isra’ila. Cohen ya jawo hankalin Guterres da cewa ai Isra’ila a 2005 ta mikawa Gaza dukkan yankin ta har ƙarshen mita. Sai dai a nan Cohen bai karisa da cewa na take kuma Isra’ila ta yi wa yankin ƙofar rago ta hanyar killace shi cikin fatara da rashin tabbas.

Shi ma jakadan Isra’ila a majalisar Gilan Erdan ya ma buƙaci Guterres ya yi murabus daga muƙamin sa don wannan matsaya ta sa.

Faɗan dai na Isra’ila da Falasɗinawa ya raba kan membobin kwamitin tsaron majalisar da akasarin su ke marawa Isra’ila baya.

Ministan wajen Falasɗinawa ya zargi majalisar da rashin ɗaukar mataki da hakan ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka a ɓangarorin biyu.

Isra’ila ta cigaba da kai miyagun hare-hare ta jiragen yaƙi kan zirin Gaza, yammacin kogin Jodan da ma cikin ƙasar Sham.

Harin ya shafi wani masallaci a nan yammacin kogin Jodan inda Isra’ila ke mamaye da shi.

Kazalika Isra’ila ta tara dakarun ta masu yawa a kan iyaka da nufin faɗawa Gaza ta ƙasa amma ta ɗan dakata da nuna cewa har yanzu akwai ɗaruruwan fararen hula a arewacin Gaza duk da dimbim mutane da su ka qaura bayan wa’adin da Isra’ila ta bayar na su fice daga yankin.

A na ganin Isra’ila na takatsantsan kar yakin na kasa ya jawo shigowar kawayen Hams daga Lebanon da Sham da zai iya zama babbar barazana.

Kai agaji ga wadanda yaki ya daidaita ya fara da motoci 20 ɗauke da magunguna, kayan kula da majinyata da dan abinci sun ketara daga Masar zuwa Gaza ta mashigar Rafah da Masar ke datsewa kirif.

Motocin dai sun shafe kwanaki su na jiran ba su damar ƙetara iyakar don kasancewar yanda Masar kan tsaurara tsaro a Rafah don hana Falasɗinawa ketarowa cikin kasar ta.

Cikin kayan akwai masakai 235 don kwantarwa waɗanda su ka samu munanan raunuka hankali don cigaba da kula da jinyar su.

Hamas a na ta ɓangaren ta ce magungunan sam ba za su wadatar ko sauya komai daga buƙatun magunguna na mazauna Gaza ba.

Kammalawa;

A nan ba abun da za a ƙarfafa da ya wuce samun adalci a duniya da kuma manyan ƙasashe masu tutiya da dimokraɗiyya da ’yanci ya dace su shige gaba wajen tabbatar da adalcin ko da hakan ya savawa muradun da su ka gaba daga kakannin su.

Rashin adalci har kullum shi ke jawo ƙaramar magana ta zama babba. Ya kamata manyan ƙasashe musamman waɗanda su ke cikin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya su zama masu gaskiya aƙalla dai ko sau ɗaya ne kan Falasɗinawa. Babba ya zama babban gaskiya ba babba da jaka ba.