Tsawon zamani, wasu ba su ɗauki ‘mace mutum ba’ saboda ta kasance mai rauni ta yadda ake mata kallon ba za ta iya komai ba sai dai kula da yara da kuma aikace-aikacen gida da dai sauransu. Akan tauye mata haƙƙin neman ilimi ko kuma bada wata gudunmuwa don cigaban al’umma tare da mayar da ita tamkar baiwa.
A mahangar addinin Musulunci, mace tana da kima sosai, sannan kuma tana da cikakken ’yancin yin duk wani abu da bai sava wa koyarwar addini ba, kama daga kasuwanci, neman ilimi da sauransu. Amma duk da wannan damar da addini ya ba mata bai hana al’umma cigaba da tauye musu haƙƙinsu ba wanda kai tsaye ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci.
Duk da wannan yanayi da mata su ke samun kansu, tarihi ya nakalto irin gudunmawar da mata suka bayar wajen cigaban addininsu a fanni ilimi, siyasa, rubuce-rubuce da sauran su. Wannan na nuna cewa ilimin mata na da gayar muhimmanci wajen cigaban al’ummar da ke tare da su da kuma addinin su. Sannan ilimi na da muhimmanci ga mace a matsayinta na uwa, saboda uwa ita ce makarantar farko ga ’ya’yanta da kuma mijin ta.
Misalin jaruman matan da suka bada gudunmuwa wajen cigaban addinin Musulunci;
(1) Sayyida Hannah mahaifiyar Sayyida Maryam (AS), ta jajirce wajen sadaukar da jaririyar ’yarta zuwa ga hidimta wa addinin Allah (SWT).
(2) Haka itama Sayyida Maryam ɗin ta yi gwagwarmayar tasowa tsakanin Yahudawan zamaninta tare da fuskantar su ba tare da tsoro ba. A lokaci guda kuma tana hidimtawa addininta har ta koma ga mahaliccinta.
(3) Sayyida Asiya (AS) matar Fir’auna (L), duk da kasancewar ta matar azzalumin sarki, bai hana ta yin gwagwarmaya, tsayuka da dakewa akan gaskiya ba duk da uquba da azabarwar da ta fuskanta a wajen mijinta, har ta samu tsira.
(4) Sannan idan mu ka yi duba a zamanin Manzon Allah (SAW) za mu ga akwai mata irin su Sayyida Khadija Bintu khuwaylid (AS), wacce ta sadaukar da dukiyar ta ga addinin Musulunci.
(5) Ga kuma ’yarta Sayyida Fatima (AS) wacce ta kasance shugabar matan duniya, ita ma ta sadaukar da komai ga addinin Allah, sannan ta tsaya kuma gefen Imam Ali (AS) wanda ya kasance miji a gurin ta, ta ba shi gudunmuwa sosai a lokacin halifancin sa.
(6) Nana Aisha (RA) matar Manzo; Ita ma ta saudar matuqa wajen cigaba addinin Musulunci, wanda hakan ya sa ake yi mata laqabi da ‘Uwar Muminai’.
(7) Sayyida Zainab (SA) ta kasance ’ya ga Sayyida Fatima(AS) ta ba da gudunmuwa tun daga yarintar ta har zuwa girmanta. Zainab ta kasance tare da xan uwanta Imam Husaini (AS) a kokarin sa na tabbatar da Musulunci da tseratar da shi daga ƙoƙarin da ake na kawar da shi da ƙarfin gaske musamman ma lokacin mulkin Yazid Ibn Mu’awiya (L). A lokacin ne Umayyawa suka tazo da dukkanin ƙarfin su wajen da wannan addinin da maishe shi ba abakin komai ba, don haka babu abinda zai ceto shi inba yunƙurin Ashura ba, kuma babu wanda zai iya gagarumin yunkurin nan inba Imam Husain (AS) ba, kuma babu wanda zai iya taimaka mai wajen cimma wannan ƙuduri inba Sayyida Zainab ba (SA). Don haka Sayyida(SA) ta ba da gagarumar gudunmuwarta wajen ƙarfafa mujahidai wajen cimma wannan yunƙuri tun kafin a zo Karbala.
Idan dai muka yi duba ga waɗanan matan za mu ga sun ba da gudunmuwa sosai ta hanya daban-daban yadda mu ma za mu iya ba da tamu iidan mu ka yi koyi da su.
Ta ya ɗabi’un mace da halayenta za su cika ta yadda za a kira ta da macen kwarai?
Na farko, samar da kyakkyawar shaksiyya ta hanyar tarbiyyatar da kanta da lizimtar siffofin mata bayin Allah salihai, misali yawaita ibada, neman ilimi, zamantakewa da al’amuran yau da kullum.
Shaksiyya: Ana so mace ta kasance tana da shaksiyya ta kwarai ta yadda kafin ta yi magana sai ta saka matuƙar tsoron Allah.
Ilimi: Mace ta kasance tana son neman ilimi duk biyu (na arabi da na zamani), saboda ba yadda za a yi addini ko gwagwarmaya ba tare da ilimi ba, a wannan vangaren dole ne sista ta dage ta qure maleji wajen sanin fannonin ilimi masu dama da kuma zurfi domin bayar da gudunmuwa mai tsoka wa addininta, idan muka duba tarihin matan da suka ba da gudunmuwa za mu ga dukansu su na da ilimi sosai.
Na biyu, gudunmuwa ga iyalenta:
Idan ba ta da aure, ya kasance za ta iya bai wa iyayenta da kuma ’yan uwanta gudunmuwa ta hanyar qarfafa zukatan su, haka ma wacce ta kasance tana da miji za ta kasance tana ƙarfafa mishi kan abubuwan da ke tasowa na yau da kullum don samun ɗaukaka adalci.
Na uku, gudunmuwa wajen tarbiyyar ‘ya’yanta da kuma kula da gidanta: tun farko sai ta kasance mai tarbiyya sannan za ta iya baiwa wasu tarbiyya, domin ita uwa ita ce makarantar farko ga ’ya’yanta, sannan ita ke tarbiyyartar da al’umma, wato a nan ta kasance kamar gonar shukar ’yan gwagwarmaya, don haka ba wani mutum da bai buƙatar tarbiyya. Sai an samu uwar kwarai ake samun ’ya’yan kwarai. Yawancin malamai da ’yan gwagwarmayar da suka shahara su na samin tarbiyya da soma karatu ne tun daga iyayensu mata,/a wannan fanni na tarbiyya mace na taka muhimmiyar rawa wajen cigaban addini.
Na huɗu, gudunmuwa ga al’umma gabaɗaya a matsayinta na uwa, ’yar uwa, yaya da kuma ƙanwa. Takan iya bada gudunmuwar ta ta hanyar Wa’azi, kula da lafiya, rubuce-rubuce, sulhu ga al’umma idan aka samu saɓanin fahimta, tallafi, matsayin malamar makaranta, ’yar kasuwa, ɗaliba da dai sauransu.
Bari mu duba waɗannan ɗaya bayan ɗaya:
Wa’azi: Mace sai ta kasance mai ilimi sannan za ta iya bada wa’azi, ilimin ta na da gayar muhimmanci, za ta iya wa’azinta ta hanyar social media, ga al’umma da ke kewaye da ita musamman idan ba su da fahimta ga gwagwarmaya.
Kula da lafiya: Karatun kiwon lafiya yana kara ba su dama wajen kula da mutanen da ke kusa da su dama hidimtawa addini, misali mu duba madubinmu wato Sayyida Zainab(SA) ta yadda ta kula da masu rauni a filin Karbala, ta ba da gudunmuwarta sosai a wannan fanni.
Rubuce-rubuce: Shima yana taimakawa wajen yaɗa hadafin gwagwarmaya, shi ma mu duba Amina Bintul Huda yadda ta ba da gudunmuwa ta hanyar rubuce-rubuce, da kuma Nana Asma’u yar Usman ɗan Fodio yadda suka bada gudunmuwa wajen rubuce-rubuce na addini. Muma zamu iya bada gudunmuwar mu ta hanyar rubuce-rubuce ta social media ko wallafa littafai.
Tallafi: Za ta iya bada tallafi ta hanyar bayar da taimakon kuɗi ko ta hanyar bayar da gudunmuwa ta hidimtawa da jikinta, misali idan wani abu na hidima ya taso ta tallafa da dukkanin ƙarfinta.
Matsayin malamar makarantar: A matsayin ta malamar makarantar nan ba akwai rawar da za ta taka ta hanyar ba su kula da nuna musu abinda ya dace.
’Yar kasuwa: ’Yar kasuwa tana bayar da gudunmuwa ga addini ta da dukiyar ta, misali Sayyida Khadija (SA) ta bada gudunmuwa da dukiyar ta, ta hanyar kasuwanci ma za ta iya bada da’awar ta da nuna gaskiya akan kasuwancin ta.
Ɗaliba: Ɗaliba zata iya bada gudunmuwarta ta hanyar zamar ma addinin ta jakadiya ta gari, ta hanyar sa cikakken hijabi, da shiga ta kamala, zamantakewar ta da abokan karatun ta, za ta iya bada da’awa ta hanyar nuna kyakkyawar mu’amalar ta da dai sauran su.
A ƙarshe dai ina kira ga ’yan uwana mata da mu tashi wajen neman ilimi, saboda ilimi na da gayar muhimmanci kuma da ilimi ne za mu iya ba da gudunmuwa ga addini, idan mu ka yi la’akarida matan da suka bayar da gudunmuwa irin su Sayyida Khadija, Nana Aisha, Sayyida Fatima, Sayyida Zainab, Amina bintul Huda, dukkansu su na da ilimi, don haka mu tashi haiqan wajen neman ilimi don bai wa addininmu gudunmawa.
Daga ZAHRA AUWAL, 09070905294 (Tes kawai).
