Mutane huɗu sun mutu a wani artabu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Aƙalla mutane huɗu ne suka mutu yayin da soja ɗaya ya ɓace a wani hari na ranar Larabar nan da ƴan bindiga suka kai a garin Tudun Bicci da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi.

Shugaban ƙaramar hukumar mulki Danko/Wasagu Honarabul Hussain Aliyu Bena ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja ta wayar tarho da cewa waɗanda suka rasu sun haɗa da jami’an gandun daji biyu da waɗansu farar hula biyu sannan kuma soja ɗaya ya ɓace yayin artabun na ranar Laraba.
A ɗaya ɓangaren kuma ya bayyana cewa da yawa daga cikin maharan sun mutu a cikin artabun yayin da waɗansu kuma sun sami raunuka daban-daban.
Ya ce wannan yankin yana fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga da ke da sansanoni a yankin jihohin Zamfara da Neja.

Honarabul Bena ya ƙara da cewa yanzu haka dai gwamnatin jihar Kebbi a wani shirin haɗin gwiwa da ƙaramar hukumar mulki ta Danko Wasagu tana ƙoƙarin ganin an shawo kan wannan matsalar ta hanyar aiki tare da jami’an tsaro da ƴan sa kai.

By ukarofi

Leave a Reply