An sallami wata jaruma daga fim bisa wallafa goyon bayan Falasɗinawa

Daga AISHA ASAS 

Wata jaruma da ta ke aikin ɗaukar wani fim mai suna ‘Scream’ ta zama korarriya dalilin wallafa saƙon nuna goyon bayanta ga Ƙasar Falasɗinu, tare da barranta kanta daga irin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Jarumar ta nuna matuƙar damuwa da halin da mutane ke ciki a Gaza, inda akai-akai ta ke wallafawa a shafukanta na sada zumunta ababen da ke wakana dangane da yaƙin Isra’ila a Gaza.

A cikin irin rubutun nata, jarumar mai suna Melissa Barrera, ta zargi Isra’ila da aikata ‘kisan ƙare dangi’ wanda ke da ƙudurin shafe wata al’umma daga doron ƙasa.

An kori jaruma Melissa Barrera, daga ci gaba da fitowa wani shiri fim mai dogon zango mai suna ‘Scream’, bayan masu shirya fim ɗin, ƙarƙashin kamfanin shirya finafinai na Spyglass, sun zarge ta da wallafa saƙonin ƙin jini Yahudawa, wanda suka ce yana daga cikin aƙidarsu rashin uzuri ga wanda ya ƙi jinin Yahudawa daidai da ƙwarar zarra.

Jaruma Melissa Barrera, wadda asalinta daga Ƙasar Mexico ce, ba ta zama irinta ta farko da aka sallama daga harkar fim sakamakon nuna goyon baya ga mutanen Gaza tare da qin jinin cin zalin da kisan ƙare dangi tare kuma bajikolin laifukan yaqi da ke gudana a Gaza ba, domin kafin ita, jaruma Susan Sarandon, wadda ta fito a fim ɗin ‘Thelma & Louise’, ita ma ta samu kanta a irin wannan korar sakamakon gabatar da jawabi da ta yi a wani taron nuna goyon bayan Falasɗinawa, wanda hakan ya yi sanadiyyar watsar da ita daga harkokin shirya finafinai.

Wani abin birgewa ga waɗannan jarumai biyu, ko guda daga cikinsu ba ta yi yunƙurin mayar da martani ba, bare har a kai ga zancen canza ra’ayinsu, zuwa ga neman afuwa kan abinda suka yarda da shi ba, duk da cewa tsakanin lokacin da lamarin ya faru, jaruma Melissa Barrera ta wallafa a shafinta na Instagram, rubutun da wasu ke ganin yana da alaƙa da maganar korar da aka yi mata.

Jarumar ta wallafa rubutu kamar haka, “Daga ƙarshe dai, na gwammace a cire ni saboda wanda na shigo da shi cikin sha’anina a kan a shigar da ni saboda wanda na cire.”