Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga ƙasar Guinea na nuni da cewa, ana zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar bayan da aka jiyo ƙazamar musayar wuta a Conakry, babban birnin ƙasar, a wannan Asabar ɗin.

Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami’an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya, ba shiga ba fita.

Wata majiya da aka sakaya sunanta ta ce, “Ana musayar wuta daga tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tare da harba makaman yaƙi a Kaloum.”

“Tun da asuba aka kulle garin, ba shiga, ba fita,” in ji wani ɗan kasuwa a yankin.

Guinea na ɗaya daga jerin ƙasashen da suka fuskanci juyin mulki tun 2020. Sauran ƙasashen sun haɗa da Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Gabon.

Shugaban sojojin juyin mulki a Guinea, Kanal Mamady Doumbouya, ya karɓe ragamar shugabancin ƙasar ne a ranar 11 ga Satumban 2021 bayan da ƙasar ta shafe shekara 11 kan turbar mulkin farar hula.