An kashe masu garkuwa da mutane da ceto mutum huɗu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

A wata arangama tsakanin wani gungun ‘yan ta’adda da sojojin bataliya ta ɗaya da ke Birnin Kebbi tare da haɗin gwiwa da ‘yan sakai sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da ƙwato mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a jejin Suru da ke jihar Kebbi.

Kamar yadda mai bai wa gwamnan jihar Kebbi shawara kan tsaro Alhaji Abdulrahman Usman ya bayyana, an yi ba-ta-kashi tsakanin jami’an tsaro tare da ‘yan sa kai da kuma ɓarayin daji a wata maɓoyarsu da ke  kan tsaunin Bangi a bayan garin Suru inda aka kashe ɓarayin kuma aka ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su.

Ya bayyana cewa wannan nasarar tana da nasaba da ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagoranacin Malam Nasiru Idris na ganin tsaro ya inganta ta hanyar baiwa jami’an tsaro goyon baya don aiwatar da ayyukansu.

Ya ƙara da cewa waɗanda aka ceto a bata-kashin da aka yi ranar Larabar da ta gabata sun haɗa da Malam Audu Fulani, 45, Umar Wakili, 14, Alhaji Iman 50 da kuma Chaggo Garba 19.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba wajen hukumar da ta fi kusa da su don ɗaukar mataki.

By Editor