Nijar: An bankaɗo sabbin bayanai kan zargin Bazoum da yunƙurin tserewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumomin shari’ar jamhuriyar Nijar sun sanar cewa binciken da suka gudanar ya bada damar gano wasu ƙarin bayanan da ke gaskanta zargin yunƙurin tserewar Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa. Sun ce sun kama kuɗaɗe da dama da wasu tarin kayayyaki a fadar ta hamɓararren shugaban.

Yayin da ya ke yin bayani a gidan talabijin ɗin RTN mallakar gwamnatin Nijar, mai shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta birnin Yamai, Salissou Chaibou, ya ayyana cewa bayanan da suka tattara sun gano cewa an ɗauki hotunan barikin dogarawan fadar shugaban ƙasa da suke zargin hamɓararren shugaban ƙasar ya tura wa Faransawa. Sannan ya ce sun bankaɗo tsarin da aka kitsa a ƙoƙarin tantance filin da jiragen sama masu saukar ungulu za su sauka su ɗauki shugaban da iyalinsa domin kai su Birnin Kebbi.

Mai shari’a Salissou Chaibou ya ƙara da cewa, binciken kayayyakin da aka kama a hannun masu yunƙurin tserewar da wanda aka gudanar a fadar tsohon shugaba Bazoum sun bada damar kama maƙudan kuɗaɗe da kadarori masu daraja, da suka haɗa da million 86,250.000 na CFA, Dalar Amurka 17,017, Euro 3,835 da Pam 5 na Ingila, CD 16 na Ghana, zinare gram 2,800, azurfa gram 333, komfitoci 3, na’urar ɗaukar hoto 1, wayoyin hannu 13, layukan waya masu yawa, da takardun filaye kimanin 25, da dai wasu wayoyi sama da 10 da aka lalata, da bindiga samfarin Bereta da sauran kayayaki.

Sannan an kama kuɗaɗe million 68 na CFA da kuɗaɗen ƙasashen waje a hannun wasu dogarawan fadar shugaban ƙasa da ake zargi da hannu a yunƙurin tserewarsa.

Wani na hannun daman hamɓararren shugaban ƙasar, Sahanine Mahamadou, da ke maida martani akan waɗannan zarge-zarge na kallon abin a matsayin yunƙurin shafa kashin kaji.

To, amma a ra’ayin shugaban kungiyar GRAZ, Gayya Salissou Amadou, na ganin bai kamata a yi gaggawar yanke hukunci kan bayanan na hukumomi ba.

A ranar 20 ga Oktoban da ya gabata ne majalisar sojoji ta CNSP ta bada sanarwar daqile yunkurin tserewar shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa, da jami’an tsaronsa biyu, har ma da masu dafa masa abinci su biyu, lamarin da ya haifar da babbar muhawara a tsakanin ‘yan ƙasar.