Daga BASHIR ISAH
Nan ba da jimawa ba ‘yan gudun hijira da ma waɗanda rikici ya ɗaiɗaita a Jihar Zamfara za su dara, biyo bayan tallafin da Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya karɓo musu daga Gwamnatin Tarayya.
Tallafin gaggawar ya ƙunshi buhunan shinkafa, katan-katan na spaghetti, garin semovita, kayan aikin gona, kekunan ɗinki, kwamfutoci, litattafan rubutu da dai sauransu.
A ranar Alhamis da ta gabata Gwamna Lawal ya kai ziyara Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Waɗanda Rikici ya Ɗaiɗaita ta Ƙasa don kyautata danganta da kuma nema wa ‘yan gudun hijira a jiharsa tallafi kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar.
A cewar Sulaiman, Kwamishinan Hukumar, Tijjani Aliyu Ahmed, shi ne ya tarbi Gwamna Lawal yayin ziyarar.
Ya ƙara da cewa, “Ziyarar Gwamna Lawal ya zuwa Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, shi ne domin samar da ƙarin hanyoyin tallafa wa waɗan matsalar ɓarayin daji ta ɗaiɗaita a Jihar Zamfara.
“Yayin ziyarar Gwamna Lawal ya roƙi hukumar da ta bai wa Zamfara fifiko duba da yadda matsalar tsaro ke ci wa jihar tuwo a ƙwarya da kuma buƙatar tallafi da take da ita. Ya kuma buƙaci da a faɗaɗa matsugunnan ‘yan gudun hijirar daga Gusau zuwa wasu sassan jihar.
“Har wa yau, Gwamnan ya jaddada buƙatar da ke akwai na yin haɗaka wajen kawar wa ‘yan gudun hijira a Zamfara su sama da 2000 wahalar da suke fuskanta.”
A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar, Tijjani Aliyu Ahmed, ya bai wa Gwamnan tabbacin hukumar za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda matsalar tsaro ta shafa a jihar da ma sauran jihohi.
Daga nan, Tijjani ya yaba da ziyarar da Gwamna Lawal ya kai masa, tare da cewa shi ne mutum na farko da ya kai masa ziyarar aiki tun bayan da shiga ofis.
Daga bisani, hukumar ta bada tallafin gaggawa don amfanin waɗanda lamarin ya shafa a Zamfara da suka haɗa buhunan shinkafa, katan-katan na spaghetti, garin semovita, kayan aikin gona, kekunan ɗinki, kwamfutoci, litattafan rubutu da dai sauransu.
