Zan daidaita komai a Man United – Erik ten Hag

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce, aungiyar na cikin wani irin yanayi amma har yanzu yana ganin shi ne mutumin da ya dace ya saita komai a Old Trafford.

Nasarar da Newcastle ta samu da ci 3-0 a gasar kofin EFL ita ce babbar nasarar da suka samu a gidan Manchester United cikin shekaru 93.

Wannan shi ne rashin nasara na takwas da United ta yi cikin wasanni 15 da ta buga, mafi muni a farkon kakar wasa tun 1962-63.

Bayan da United ta sha kashi a hannun Manchester City a ranar Lahadi, shi ne karo na farko da United ta yi rashin nasara a wasannin gida da ci uku ko fiye da haka tun watan Oktoban 1962.

“Na fahimci cewa wannan sakamakon bai yi masu daɗi ba kuma dole ne su yi ƙorafi,” inji shi.

“Amma ina da yaƙinin cewa zan iya, a halin yanzu muna cikin wani mummunan yanayi kuma alhakin haka ya rataya a wuya na”.

United za ta kara da Fulham a wasanta na gaba a gasar Firimiya a ranar Asabar mai zuwa.

By Editor