Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin harin ta’addanci a Kano

Daga BASHIR ISAH

Jami’an tsaro a Jihar Kano sun samu nasarar daƙile yunƙurin harin ta’addanci da Boko Haram ta shirya kaiwa a yankin Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar.

Sojoji da DSS ne suka daƙile wannan yunƙuri a ranar Juma’a, tare da kama wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne.

Cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun sojoji, Onyema Nwachukwu ya lissafo wasu makamai da suka ƙwace da suka haɗa da bindiga ƙirar AK 47 guda biyar, bindigar harba roka ɗaya, bom samfurin RPG guda shida, rigunan aiki na sojoji da dai sauransu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rundunar haɗin gwiwa ta sojoji da DSS ta yi nasarar daƙile yunƙurin harin ta’addanci a Kano a wani samame da jami’ai suka kai a maɓuyar ‘yan ta’adda a yankin Ƙaramar Hukumar Gezawa da safiyar Juma’a, 3 ga Nuwamban 2023.”

“An kai samamen ne da nufin bankaɗo shirin kai harin ta’addanci daga wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne a Jihar Kano.”

Onyema Nwachukwu ya ce nasarar da aka samu manuniya ce dangane da kyakkyawar zumuntar aiki da ke tsakanin sojoji da DSS.