Bikin Magaji bai hana na Magajiya: Matsin tattalin arzikin Nijeriya bai hana Tinubu canza wa matarsa motoci ba 

Daga AMINA YUSUF ALI 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana, zai saya wa matarsa Remi motocin Naira biliyan 1.5, kuma shi ma zai sauya motocin ofishinsa da Naira biliyan 2.9.

Duk da matsalar rashin kuɗdi da tsadar rayuwar da ake ta kuka, wadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ya jefa ‘yan Nijeriya bayan cire tallafin fetur, Tinubu zai sai wa Remi matarsa  motocin Naira biliyan 1.5, shi ma zai sauya motocin ofishinsa da Naira biliyan 2.9.

Waɗannan Naira biliyan 2.9 kuwa, Gwamnatin Tinubu za ta kashe su ne wajen maye danƙara-danƙaran motocin Ofishin Shugaban ƙasa, waɗanda aka ci zamanin mulkin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Wannan adadin kuɗaɗen suna cikin  Kasafin 2023 na ƙarshen shekara, wanda Tinubu ya aika Majalisa domin amincewa.

Suna cikin kasafin na Naira tiriliyan 2.17 da ya aika Majalisar Dattawa a ranar Talata domin amincewa.

A ranar Litinin ce dai Majalisar Zartaswa ta ƙasa ta amince a kashe kuɗaɗen domin gaggauta aiwatar da wasu ayyuka masu matuqar muhimmanci ga ƙasa.

Shugaba Tinubu da manyan jami’an gwamnatinsa har yau ba su daina roƙon ‘yan Nijeriya su ƙara haƙuri da juriyar ɗanɗana raɗaɗin tsadar rayuwar da su ke fama ba, tun bayan rantsar da Tinubu, watanni biyar da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa,  gwamnatin Tinubu ta haukace tuburan wajen ragargazar maƙudan kuɗaɗen da ya kamata a yi wa ‘yan Najeriya ayyukan raya ƙasa da su.

A gefe ɗaya kuma su na roƙon ‘yan Najeriya su ci gaba da sadaukar da kansu talauci da raɗaɗin tsadar rayuwa na ci gaba da kwankwatsarsu.