Atisaye: Babu buƙatar jama’a su tada hankulansu – NAF

Rundunar Sojan Sama (NAF) ta yi kira ga ‘yan ƙasa kan cewa kada su firgita ko tada hankalinsu da ganin jami’anta bajaja a kan hanyoyi a sassan ƙasa a ranar Asabar.

Daraktan Yaɗa Labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, gudun sassarfa na shekara-shekara na tsawon kilomita 10 da suka saba yi, na bana zai gudana ne a ranar Asabar, 4 ga Nuwamban 2023 da misalin ƙarfe 6.00 a Abuja da sauraran sassan ƙasa inda ake da sansanonin rundunar.

Sanarwar ta ce, “Ana shawartar al’umma musamman masu abubuwan hawa da waɗanda ke zama a yankin AYA da Asokoro, da sauran mazauna kusa da inda ake da sansanonin NAF a sassan ƙasa cewa, kowa ya ci gaba da harkokinsa ba tare da fargaba ba.”

Gabkwet ya ce atisayen ɓangare ne na ƙoƙarin da NAF ke yi domin ci gaba da ingata lafiyar jami’anta.

Ya ce atisayen Abuja zai kankama ne daga barikin NAF, Asokoro zuwa shataletalen Hedikwatar Tsaro zuwa hanyar Keffi/Kugo zuwa shingen bincike da ke Kugbo, sannan a ƙarasa a ƙofa ta biyu ta barikin NAF, Abuja.

Ya ƙara da cewa, yayin wannan atisayen za a taƙaita zirga-zirgar abubuwan hawa a waɗannan yankuna.

Ya ce atisayen a sauran sassan ƙasa zai shafi manyan hanyoyi da ke kusa da sansanonin NAF da kewayensu, tare da cewa an ɗauki ƙwararan matakai domini tabbatar da ba a samu cunkosu ba yayin atisayen.