Ƙaramin kasafin kuɗi: Sojojin ruwa sun shafa wa Tinubu kashin kaji

Spread the love

*Ban buƙaci yin ta-more ba, inji Shugaban Ƙasa
*Majalisa ta fizgo wa ɗalibai biliyan N5 daga Fadar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daga dukkan alamu wani ɓangare na ƙaramin kasafin kuɗin da Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya ta nemi a ba ta cikin ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na 2023, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa Majalisar Dokoki, domin neman amincewarta, ya nemi ya shafa shugaban kashin kaji a wajen akasarin masu sharhi da lura da al’amuran yau da kullum a faɗin ƙasar, saboda yadda cece-kuce ya ɓarke akan batun har ma Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu kan lamarin.

Wannan ya biyo biyo bayan yadda aka nemi Majalisar Dokokin ta amince da kashe zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan Biyar, don sayen jirgin ruwa ga Shugaban Ƙasa daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke cikin ƙuncin rayuwa, lamarin da ya janyo cece-kuce da tir a faɗin ƙasar.

Biyo bayan hakan, nan da nan sai Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa ’yan ƙasar cewa, bai shirya yin ta-more da kuɗin ’yan ƙasa ba a cikin ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na 2023, saɓanin bayanan da aka riƙa yaɗawa a baya-bayan nan.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Tope Ajayi ne ya bayyana hakan, inda ya yi ƙarin haske da cewa, Shugaba Tinubu bai nemi a saya masa jirgin ruwan Fadar Shugaban ƙasa ba kwata-kwata.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna ɓacin rai bayan da aka bayyana cikakken bayanin ƙarin Naira Tiriliyan 2.1 da shugaban ya miƙa wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, domin amincewa.

A cikin kasafin kuɗin, an ware Naira Biliyan 5.09 na jirgin ruwan Fadar Shugaban Ƙasa, Naira biliyan 2.9 na sababbin motocin Fadar Shugaban Ƙasa da kuma wasu Naira biliyan 2.9, don maye gurbin ababen hawan motsa jiki da ke aiki a fadar.

Sai dai kuma kasafin kuɗin jirgin ruwan an saka shi ne a ƙarƙashin shirin da Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya ta yi na kashe maqudan kuɗaɗe har Naira biliyan 42.3, inji Fadar Shugaban Ƙasar, amma ba kai-tsaye ne Shugaban Ƙasa ya nemi a saya masa jirgin ruwa ba.

Tope ya ce, “mun ji abubuwan da ke faruwa a kafafen sada zumunta. Yana da muhimmanci a bayyana a fili cewa, Shugaba Bola Tinubu bai nemi jirgin ruwan Shugaban Ƙasa ba, kuma Ina shakkar idan zai buƙaci jirgin ruwa, domin ayyukan ofishinsa.

“Daga abinda na sani shine, buƙatun jirgin ruwa daga Rundunar Sojan Ruwa ne, kuma dole ne su na da dalilan da ya sa suke buƙatar shi.

“Ya kamata ma’aikatar kasafin kuɗin ta kasance tana iya bayyana wa al’umma dalilin da ya sa za a yi amfani da irin waɗannan kuɗaɗe a yanzu duba da yanayin tattalin arzikin ƙasa.”

Ajayi ya cigaba da cewa, “yana da kyau a ce aikin jarida ya ƙara wayar da kan jama’a, kada ya haifar da yanayi na saɓani, ba daidai ba ne a danganta duka tanadin kasafin kuɗi ga Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa ba.

“Lokacin da fadar gwamnati ta yi tanadin ababen hawa, sai a ce wai Shugaban Ƙasa ne zai yi amfani da dukkan motocin ko kuma ya ci abinci shi kaɗai, idan an yi tanadin abinci.”

Majalisar Wakilai:

Majalisar Wakilan Nijeriya ta mayar da ƙudirin buƙatar sayen jirgin ruwa na Shugaban Ƙasa zuwa tsarin rancen ɗalibai na Gwamnatin Tarayya, inda hakan ya ƙara ɗaga rancen Naira biliyan 5.5 zuwa Naira biliyan 10 a cikin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023.

Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Honarabul Abubakar Kabir Bichi, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan amincewa da ƙarin kasafin kuɗin.

“Idan za a iya tunawa, lamunin ɗaliban ya kai Naira biliyan 5 a cikin kasafin kuɗin, amma mun ƙara shi zuwa Naira biliyan 10,” inji shi.

An ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta gabatar da audirin ware naira biliyan 5.095 domin sayen jirgin ruwan shugaban ƙasa a cikin shirin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023.

Sai dai Bichi ya ce, kwamitin ya kuma kara kasafin kudin ma’aikatar tsaro daga Naira biliyan 476 zuwa Naira biliyan 546 sakamakon matsalolin tsaro.

Ya kuma bayyana cewa an yi la’akari da mafi ƙarancin albashin ma’aikata tare da amincewa da miƙawa ɓangaren zartarwa na gwamnati tare da yin alƙawarin sa ido kan yadda ’yan majalisa za su tabbatar da aiwatar da kashi 100 cikin 100.

Tun da farko dai majalisar ta amince da karin naira tiriliyan 2.18 na kasafin kuɗi na shekarar 2023 da gwamnatin tarayya ƙaraashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta buƙata.

Hakan ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin kasafin kuɗi da kwamitin samar da kayayyaki wanda kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya jagoranta a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Rahoton ya karkata zuwa ga; “Ƙudirin dokar da zai ba da izini ga batun daga haɗaɗɗiyar asusun tattara kuɗaɗen shiga na tarayya jimillar Naira 2,176,791,286,033 na shekarar da za ta ƙare 31 ga Disamba 2023”, Honarabul Abubakar Kabir Bichi ya gabatar da shi. 

Shugaba Tinubu ya bayyana a wata wasiqa da kakakin majalisar Tajudeen ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata an nemi a gaggauta zartar da ƙudurin ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2023 don baiwa gwamnatin tarayya damar samar da ƙarin kuɗaɗen tallafi da sauran ayyuka.

Saboda haka, an yi la’akari da lissafin kuɗi don karatu na biyu kuma an zartar da shi kuma aka miqa shi ga kwamitin kasafin kuɗi don ci gaba da aiwatar da doka.

Amincewa da ƙaramin kasafi:

Majalisar Dokoki ta Nijeriya (Dattawa da Wakilai) a jiya Alhamis sun amince da ƙudirin ƙarin kasafin kuxi na Naira tiriliyan 2.17 na shekarar 2023 bayan karatu na uku.

Kafin zartar da ƙudirin, Majalisar Dattawa ta amince da rahoton zaman da aka yi na daidaita zaman majalisar dattawa da ta wakilai a kan ƙudirin kasafin kuɗin na shekarar 2023 kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi, Sanata Solomon Olamilekan Adeola (APC Ogun ta Yamma) ya gabatar.

Ƙudirin ya tsallake karatu a dukkan majalisun biyu kamar yadda ‘yan majalisar suka ce yana da amfani ga ƙasa.

Shugaba Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dokoki ta Qasa neman amincewar N2,176,791,286,033 a matsayin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023 don magance gyare-gyaren albashin ma’aikata, tsaro da sauransu.

Shugaban ya kuma aike da tsarin kashe kuɗi na matsakaicin wa’adi na 2024-2026 (MTEF) da Takardar Kuɗi na Kasafin Kuɗi zuwa ga majalisun tarayya guda biyu.

Kwanan nan, Majalisar Dattijai ta amince da Naira biliyan 819 wajen samar da wani ƙunshin tallafi na Naira biliyan 500.

Tinubu ya ce ƙarin ƙudirin ya zama dole domin qarin matakan jin daɗi da suka haɗa da bayar da albashi. Majalisar zartaswa ta tarayya da shugaban ƙasa ya jagoranta a ranar Litinin ta amince da ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 2.1.

A ranar Talata ne ‘yan majalisar suka fara muhawara kan gaggawar zartar da ƙarin kasafin kuɗin. ‘Yan majalisar sun bayyana buƙatar musamman inganta muhimman buƙatun jama’a da kuma wuraren gaggawa da suka haɗa da samar da ababen more rayuwa, rashin tsaro, buƙatun ma’aikata (biyan albashin Naira biliyan 210 na albashi da kuma (rancen ɗalibai Naira biliyan 5.5).

By Editor