Duniya mai yayi: Mawakan Kannywood sun yi wa Rarara taron dangi akan Buhari

Spread the love

Daga WAKILINMU

Wasu fitattun mawaqan masana’antar Kannywood a ƙarƙashin ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya sun caccakin fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, bisa sukar da ya yi wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Babban abin mamakin shine, yawancin mawaƙan da suka taso su na caccakar Rarara ɗin ba su tare da tsohon shugaban ƙasar a lokacin da ya ke gadon mulki, yayin shi kuma Rarara ɗin yana tare da Buhari har zuwa lokacin da ya sauka daga kan karagar mulki.

Rarara ya janyo waccan magana ne a makon jiya, inda ya kira taron manema labarai ya caccaki tsohuwar gwamnatin, inda ya ke kwanaki 100 na gwamnatin shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu, ta fi shekara takwas din ta Buhari.

A ranar Larabar da ta gabata ne ƙungiyar Murya Ɗaya a ƙarƙashin jagorancin fitaccen mawaqi Ali Jita a birnin Kano, wanda ya ce, su mawaƙan Arewa su na girmama magabata. Don haka kada a danganta su da abinda Mawaƙi Rarara ya faɗa.

A yayin da ya ke ƙarin haske kan lamarin, fitaccen mawaƙi Ado Gwanja ya ce, abinda ya sa suka ga dacewar su fito su yi wa duniya bayani shine, saboda yadda suka ga har wasu magauta sun fara yi musu kuɗin goro da Rarara, don haka tilas su barranta da shi.

Fitattun mawaƙa da dama dai sun samu halartar taron manema labaran a wannan rana.

By Editor