Nijar ta nemi Togo ta shiga tsakani a rikicinsu da ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin sojan Nijar ta nemi Shugaban Ƙasar Togo, Faure Gnassingbe ya shiga tsakani a tattaunawa da ƙasashen duniya musamman ma Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma (ECOWAS) wadda ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi tun bayan juyin mulki.

Ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da Shugaba Gnassingbe a Lome babban birnin ƙasar ranar Litinin. Ya kuma nemi Togo ta tsayawa Nijar a yarjejeniyar janye sojojin Faransa daga ƙasar ta yankin Sahel.

“Yana da muhimmanci a koyaushe mu tunatar da abokan kawancenmu cewa, ƙofar Nijar a buɗe take, ko da an yi kulle-kullen da ba za mu iya magana da abokan hulɗarmu ba,” Mody ya shaida wa manema labarai bayan kammala taron.

Ƙungiyar ECOWAS ta sanya wa Nijar takunkumin tattalin arziƙi da kuma rufe harkokin kasuwanci na kan iyaka da Nijar a yunƙurin matsa wa shugabannin ƙasar lamba har sai sun mayar da mulkin dimokraɗiyya.

Togo, duk da kasancewarta mamba a ƙungiyar Ecowas, ta ɗauki wasu matakai na haɗin gwiwa da shugabannin sojojin Nijar tare da bayyana aniyar hawa teburin tattaunawa.

Tuni dai Faransa ta fara janye dakarunta 1,500 daga Jamhuriyar Nijar, bayan da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta buƙaci su fice jim kaɗan da hamcarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 28 ga watan Yuli.
Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey ya ce ƙasarsu a shirye take ta taimaka wajen tattaunawa.

“Togo na adawa da duk wani matakin juyin mulki,” in ji shi. “Amma a yanayi na musamman na ƙasarku, Togo ta fahimta, kuma tana son taimaka muku,” in ji ministan.

Shugaban Nijeriyar, Bola Tinubu, wanda kuma shi ne jagoran ECOWAS, ya bayyana taka-tsantsan wajen mu’amala da Nijar saboda damuwar da ake da ita dangane da hamɓaras da Shugaba Bazoum daga kan mulki.

Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta ce za ta miqa mulki bayan shekara uku hannun farar hula, yayin da ƙungiyar ECOWAS ta buƙaci a gaggauta mayar da aiki da tsarin mulki.

Duk da haka, ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya don ganin a shawo kan lamarin.