Gwamnan Oyo ya yi wa ma’aikata ƙarin Naira 25,000 a kan albashinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ma’aikatan jihar da ‘yan fansho za su riqa karɓar tallafin kuɗi na Naira 25,000 da kuma N15,000 duk wata na tsawon watanni shida har sai an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Ya kuma jaddada muhimmancin ma’aikata da al’ummar jihar wajen haɗa hannu da gwamnatin jihar domin bunƙasa tattalin arzikin jihar na tsawon lokaci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan a ofishin gwamna, Sakatariya, Agodi a Ibadan.

Ya yi nuni da cewa duk da cewa gwamnatinsa za ta so ta yi aikin da za a riƙa tunawa da su shekaru da dama bayan ya bar mulki, za ta ci gaba da kula da jin daɗin ma’aikatanta.

Za a biya kuɗaɗen tallafin ne na tsawon watanni shida masu zuwa, wanda hakan zai sa a samu ƙarin Naira biliyan 2.2 a kan lissafin albashin ma’aikata na wata-wata.

Gwamnan ya cimma yarjejeniya da shugabannin ƙwadago domin aiwatar da wannan shiri.